♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦ MANUFAR KATIN JIBWIS™  ♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦♦

A ranar 18-20 jan 2013 wadda yayi daidai da 6-7/safar/1434 kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta gabatar da wata lacca a garin sokoto wadda ta gayyaci dalibai da sukayi karatu a jami’oi na musulunci na duniya don su gabatar da laccoci tare da baiwa wannan kungiya shawara akan yadda zata ci gaba.
Akwai laccoci guda biyar daga ciki
wanda sunyi tasiri matuka wajan
yadda jibwis zata habaka:

” ﺍﻟﻤﺆﺳﺴﺎﺕ ﺍﻟﺪﻋﻮﻳﺔ: ﻣﻔﻬﻮﻣﻬﺎ , ﻛﻴﻔﻴﺔ ﺇﻧﺸﺎﺋ
ﻬﺎ , ﺇﺩﺍﺭﺗﻬﺎ ﻭﻣﻘﻮﻣﺎﺕ
ﻧﺠﺎﺣﻬﺎ ”
“- ﺍﻟﻌﻼﻗﺔ ﺑﻴﻦ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﺇﺯﺍﻟﺔ ﺍﻟﺒﺪﻋﺔ ﻭﺇﻗﺎﻣﺔ ﺍﻟﺴﻨ
ﺔ ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﺪﻋﺎﺓ ﺍﻟﺨﺮﻳﺠﻴﻦ
ﻓﻲ ﺍﻟﺠﺎﻣﻌﺎﺕ ﺍﻹﺳﻼﻣﻴﺔ ﺍﻟﻤﺨﺘﻠﻔﺔ ) ﺍﻟﻮﺍﻗﻊ ﻭﺍﻟ
ﻤﺄﻣﻮﻝ”(
“- ﺩﻭﺭ ﻃﻼﺏ ﺍﻟﺠﺎﻣﻌﺎﺕ ﻓﻲ ﻧﺠﺎﺡ ﻭﺗﻄﻮﻳﺮ ﺍﻟﻌﻤ
ﻞ ﺍﻟﺪﻋﻮﻱ ﻭﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻤﻲ ﻓﻲ
ﺍﻟﻌﺼﺮ ﺍﻟﺤﺎﺿﺮ”
“- ﺷﺒﻜﺔ ﺍﻟﻤﻌﻠﻮﻣﺎﺕ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﺔ ﻭﺍﻟﺪﻋﻮﺓ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﺗﻌﺎﻟﻰ”
“- ﺍﻟﺠﺎﻧﺐ ﺍﻹﻗﺘﺼﺎﺩﻱ ﻓﻲ ﺣﻴﺎﺓ ﺍﻟﺪﺍﻋﻴﺔ ﺍﻹﻓﺮﺍﻁ
ﻭﺍﻟﺘﻔﺮﻳﻂ ”

A laccar da Dr. Abubakar Muhammad Abubakar ya gabatar ya kawo hanyoyi da duk wata kungiya ta musulunci tayi amfani dasu zata ci nasara da ikon Allah, daga ciki ya kawo hanyoyi goma, Amma zamu kawo biyu daga ciki:
1. Ya zama kungiya tana da dukiya isasshiya kuma mai dorewa dan dogaro da kanta tare da lissafi mai tsari.
2. Samarwa kungiyar daraja a idon yayanta da kishiyoyinta.
Lallai dogaron kungiya kullum akan bara da kyauta abune mai zubar da mutuncin kungiya, domin kungiyoyin musulunci na duniya irinsu: ‎ﺭﺍﺑﻄﺔ
ﺍﻟﻌﺎﻟﻢ ﺍﻹﺳﻼﻣﻲ , ﺍﻟﻨﺪﻭﺓ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﺔ ﻟﻠﺸﺒﺎ
ﺏ ﺍﻹﺳﻼﻣﻲ , ﺍﻟﻤﻨﺘﺪﻯ ﺍﻹﺳﻼﻣﻲ .
Da sauransu suna da hanyoyin neman taimako ta yadda idan sun samu taimakon zasu koma dogaro da kansu.
Kuma ya kamata mutane su gane cewa wannan kungiya bata hana
neman taimako ba, sai dai ya kasance ta hanyar da bazai zubar da mutuncin kungiyar ba. Wannan
kungiya tayi bincike mai tsawo kafin ta fito da katin JIBWIS, domin shine hanya da idan akayi amfani dashi zai biya bukatar wannan kungiya ta yadda zata iya dogaro da kanta har ta iya taimakon wani.
Wannan kungiya ta futo da hanyar tallafawa marayu da gajiyayyu wadda tayi nisa akai, kuma ansamu nasara wacce bata kirguwa. Kuma wannan katin bana shiga kungiya bane kamar
yadda wasu suka zata, hanyace
kawai da wannan kungiya take gani akwai nasara da ikon Allah.
Alhamdulillah wannan kungiya tana da jarin malamai na dukkan mataki da masallatai da makarantu, abinda ya rage mata shine yadda zata rinka samun hanyar gudanar dasu, to Yanzu
muna ganin Allah ya kawo lokacin, don wannan tsarin kati yayi nisa, kuma mutane suna bayar da hadin kai yadda ya kamata. Kuma wannan tsarin
kati yana da hanya ta kiyaye duk
abinda aka taimaka dashi yadda babu abunda zai salwanta da ikon Allah.
Allah shi taimake mu baki daya… Ameeen.

«Jibwis Taraba»

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s