Dan Izala dai bai yarda da ko daya daga wadannan ba, shi a ganinsa qaunarsa da Annabi SAW yake ganin Annabin….

KU ZO MU BIDO AMSA.
(1)Sun ce Imamansu duka da mabiyansu shiryayyu ne, amma mutanen Annabinsu batattu ne.
(2)Matan Imamansu da ‘ya’yansu iyalan gidansu ne, amma matan Annabinsu da ‘ya’yansa ba na sa ba ne.
(3) Matan Imamansu kintsattsu ne, kuma na gari ne, Amma na Annabinsu maha’inta ne kuma ba kamammu ba ne.
(4) Dole a tabbatar da cewa sun ci nasarar isar da saqon Ahlul Baiti, kuma Allah ya amince da su, amma Annabi tun yana da rai aka juya masa baya, duk dubun dubatan da suka yarda da shi sun koma sai mutum 4.
(5) Duk wadan da suka yi yaqi suka musluntar da qasashensu kafurai ne, su da aka musluntar din su ne musulman gaskiya.
(6) Wadan da suka zauna tare da Annabi cikin tsanani da sauqi, suka yi yaqin musuluntar da jama’a duk kafurai ne, ajamawan da ko Larabci ba su iya ba su ne mutanen qwarai.

Dan Izala dai bai yarda da ko daya daga wadannan ba, shi a ganinsa qaunarsa da Annabi SAW yake ganin Annabin:-

1) Gwani ne wajen zaben abokan tafiya.
2) Tsarkakakke ne ya sa Allah ya ba shi mata na gari.
3) ‘Ya’yansa ba agololi ba ne na sa ne, su da matansa duk iyalinsa ne.
(4) Maganar da Allah SW ya yi ta cewa ya cika addini, Annabinsa ya ce a shaida ya isar gaskiya ce.
(5) Kuma barin saqonsa da komawa na qarya sam sahabbansa ba su yi ba, wadancan ma sun shaida cewa ba su yi ba.
To ku masu da’awar son Annabi, shin kuna tare da waye?

(Baban Manar Alqasim)

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s