A ranar Talata ne shafin Facebook ya cika shekaru 10 da kafuwa; sai dai wasu na hasashen cewa tauraruwarsa za ta fara dusashewa.

Yawancin matasan da ke amfani da Facebook sun kwatanta shi da cuta mai yaduwa
Idan dai har hasashen wani bincike da aka gudanar kwanan baya ya tabbata, to lallai za a iya cewa kasuwar Facebook na fuskantar barazana. Rahotanni da dama sun nuna cewa akasarin masu amfani da shafin — matasa — sun kosa da yadda shafin yake.
Wani bincike ma ya kwatanta Facebook da cututtuka masu yaduwa.
Kafafen watsa labarai na duniya dai sun wallafa irin wadannan rahotanni, yawanci tare da hoton mutumin da ya mallaki Facebook, Mark Zuckerberg, ya sha mur.
Wani rahoto ya nuna cewa an samu karuwar kashi 80 cikin 100 na mutane masu shekaru 55 zuwa sama da ke amfani da shafin
A lokacin da masu bincike daga jami’ar Princeton suka yi amfani da shafin matambayi-ba-ya-bata na Google inda suka yi hasashen cewa Facebook zai rasa kashi 80 cikin 100 na masu amfani da shi nan da shekaru uku masu zuwa, shafin ya mayar da martani mai zafi.
Kodayake wani rahoto ya nuna cewa kashi 25 cikin matasa da ke amfani da Facebook sun daina amfani da shi, amma wani binciken ya nuna karuwar kashi 80 na mutanen da ke da shekaru 55 zuwa sama suna amfani da shi.
Don haka hasashen da ake yi cewa Facebook zai rasa kaso mai yawa na masu amfani da shi ba zai razana Mark Zuckerberg ba, musamman saboda kudin shigar shafin na karuwa.
A yanzu dai shafin na Facebook, wanda aka fara a Jami’ar Harvard da ke Amurka, yana da mutane biliyan 1.23 da ke amfani da shi.
Kudin shigar kamfanin ya haura da 55% zuwa $7.87bn a 2013, sannan ribarsa ta nunka sau bakwai, lamarin da ya sa a yanzu yake da fam£1.5bn.
Ko ma dai me zai faru da Facebook, abin da ya fito fili shi ne: shafin ya zama kundin adana tarihin al’uma.

(BBC Hausa)

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s