SAKON TA’AZIYYA GA DAUKACIN MUSULMAN KASARNAN NA RASUWAN MARIGAYI SHEIKH AUWAL ADAM ALBANI ZARIYA DA IYALANSA.

KUNGIYAR JAMA’ATU IZALATIL BIDI’AH WA IQAMATIS SUNNAH TA KASA TANA MIKA SAKON TA’AZIYYAR TA GA DAUKACIN MUSULMAN KASARNAN NA RASUWAN MARIGAYI SHEIKH AUWAL ADAM ALBANI ZARIYA DA IYALANSA.
Sakon ta’aziyyar ta fito ne daga bakin Ash-Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau (Shugaban Kungiyar ta kasa) yayi juyayi kwarai da gaske ga irin yadda akayiwa wannan shehin Malami kisan gilla tare da matarshi da dansa, basu ji ba basu gani ba.
Yaci gaba da cewa daya daga cikin magabata yanacewa “damaison kashe wani zayyi hakuri da zaimutu batare da ya kashe shiba, ka kashe kudinka ka wahalar da kanka ka bata lokacinka ga kuma ‘Diban zunubi wurin kasheshi”
(“waman yaqtul mu’minan muta ammidan fajaxa uhu jahannam khalidan fiha…”).
Insha Allahu Marigayi Sheikh Auwal Adam Albani yayi kyakkyawan karshe, Muna kuma yi masa Addu’an Allah ya Amshi Shahadarsu, Ya kyautata Makwancin su. “Inji Shugaban”
Daga karshe yayi kira ga dukkan daukacin Musulmi da mu dage da Addu’oi, Yace Dukkan Abin da yafi karfin mu baifi karfin Allah ba, Allah ya tona asirin Duk wani mai hanu a cikin kashe Malaman Addini da ake yi ba dare ba rana a wannan kasa tamu, Shugaban yayi addu’oi masu yawan gaske kan Allah ya gafartawa Marigayin tare da Iyalansa.

(Jibwis Nigeria)
http://www.jibwisnigeria.org

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s