“SIYASA TAFI SALLAH – JEFA QURI’A TA FI SALLA – SIYASA TA FI AIKIN HAJJI!”Babban abin da ya yi ta yawo a bakin wasu daga cikin masu fadi a ji a wannan matattara ta mu ta Arewa shi ne, wasu kalamai ne da aka ce sun fito da wannan siga ta sama daga bakin Dottijo kuma babban girandi-kadinnan, wato malamin nan na Nigeria kuma daya daga cikin mambobin majalisar malamai da fatawa na Duniya, wato Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.

Ance in mafadin magana wawa ne ai majiyinta da sauran hankalinsa.
Babban abin da ya yi ta yawo a bakin wasu daga cikin masu fadi a ji a wannan matattara ta mu ta Arewa shi ne, wasu kalamai ne da aka ce sun fito da wancan siga ta sama daga bakin Dottijo kuma babban girandi-kadinnan, wato malamin nan na Nigeria kuma daya daga cikin mambobin majalisar malamai da fatawa na duniya, wato Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.
Masu fashin baqi dai sun tabbatar da cewa wadancan lafuzza tuni sun fitar da shi a muslunci, galibin riddantar da shi ma ya fi qarfi ne bayan rasuwarsa, kenan ba bu sauran wata hanyar tuba, don kuwa aikin hajji rukuni ne, sallah kuma ita ce mafi girman Ibada.
To abin da ya bayyana dai wannan matattara ta mu tana da yawan kimtse idanunta alhali tana da buqatar ganin fitintunin da suke gabanta, da haka ne wata maqarqashiya ta kunno kai daga qarshin qasa yadda aka sanya shirye-shiryen zabe lokacin ibadar Allah, ga dubannin musulmi za su bar qasar zuwa qasa mai tsarki, nan fa masu hangen nesa suka gano wannan manaqisar, Marigayi Sheikh Gumi ya fadakar da mutane cewa in fa musulmi ya rasa damar hayewa karaga, to fa ibadar zuwa sauke faralin ma ba samuwa za ta yi ba.
Haka a kwashe jiki gaba daya a shiga masallaci, alhali ga ‘yan aringizo a tsattsaye lokacin jefa quri’a shi ma kuskure ne, don in mai kallon Gabas ya fadi, sallar ma ba za ta samu ba, kenan matsayin jefa quri’a a lokacin ba qarami ne ba, bayanan malam a yau duk sun gama bayyanuwa, kamar dai yadda na karanta wani littafi wai shi “Jiki magayi”.
To bayan wasu ‘yan shekaru sai kuma na sake jin wata fatawa a daidai lokacin zabe, in da wani mai hangen nesa shi ma da irin na sa madubin, yana gaya wa mabiyansa cewa, da su dangwala wa mai kallon Gabas gwara dai mai aljuhun baya, ba don komai ba wai don mai kallon Gabas din yana zagin shugabaninsu, shi kuwa mai aljuhun bayan bakinsa alaikum, haka dai wannan fatawar ta yi ta kodi a tsakanin mabiya har ta kifar da wannan al’ummar, sai daga baya aka fahimci cewa malam dai ya yi asarar mabiya masu dimbin yawa qarqashin karkatacciyar fatawa irin ta sa, to amma ko a jikinsa tun da ba abin da ya shafi gidansa, hasali ma ga hedikwatar jam’iyya ta qara fitowa sarari.
Abin takaici, kasuwar bara ta yi kwantai, ga ta bana ana sake qoqarin baje kolin kifar da al’umma ta hanyar kautattun fatawowi, kenan darasin da muka dauka cikin shekarar bara ko kadan ba mu fahimci komai ba, sai maimaita fatawar Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi muke yi, wace aiki da ita ya tsamar da miliyoyin masu ruku’i da sujada, muka bar jaki muka kama dukan taiki, ga abin zargi nan a tsakaninmu shi ya janyo fitintinu mun bari muna qoqarin aibanta wanda ya tsamar da jama’a daga nutsa a mahallaka.
Ya Allah kar ka kama mu da abin da wadancan suke aikatawa, ga shi qarara muna dandana kudarmu amma ana qara ingiza mu rami.

(Jibwis Nigeria)

Advertisements