Wai Malam yayi rantsuwa akan wani mawaki wai yana wuta in kuma ba haka bane Allah ya chanja masa Halitta – Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe. (Secretary General Of Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah Nigeria)

A ‘yan kwanakin nan ne Wasu Masu yada jitata maras asali sukayi ta yada jita jita wai Malam yayi rantsuwa akan wani mawaki wai yana wuta in kuma ba haka bane Allah ya chanja masa Halitta, to kuma sai sukace wai Allah ya chanja masa Halittar. Wannan Zance Karya ne tsagoranta, Duk wanda yaje Wa’azin kasa da aka gabatar a garin Anka a asabar da lahadin da suka gabata wato 18/19 ga watan february yaga Malam lafiya Lau kuma ya gabatar da wa’azi mai tarun ilimi da basira, a lokacin da aka gabatar da shi zai hau mumbari yayi wa’azi, kazo kaga ikon Allah Malam, kiran sunansa. tafiyarsa, hawa mumbarin sa, da sallamarsa duka kabbara ake ta faman yi kamar garin zai fashe, saboda anyi masa ne dan a kaskaskantar da shi Allah kuma ya kara daga darajar sa a dalilin hakan.
Ni wakilin Jibwis Nigeria Ibrahim Baba Suleiman ina tare da shi a mota daya zuwa Anka da dawowa, Mun tsaya a garin Funtua zamu ci abinci Kafin mu kare cin abincinnan kawai sai ‘yan uwa masu kaunar Malam sukayi ta hawa Babur da mota kawai dan suga Malam musamman dan su kara tabbatar da jita jitar da ake ta yadawa, kofar gidan da mukazo ya cika makil da mutane, can na hango wani matashi ya tinkaro Malam koda ya iso sai yace Malam ashe lafiya lau kake ana ta maka sharri wai Allah ya chanja maka Halitta, Malam sarkin murmushi, nan take yayi murmushi yace to yanzu ya ka ganni?
A kullum in kaga irin wayoyin da nake amsawa daga ni har Malam din ganin kusanci na da shi daga sassan duniya ana ta tambayar mu wai gaske ne Allah ya chanja wa Malam Halitta, ni kuma bana gajiya nakanyiwa kowa bayanin cewa karya ne.
Dana tambayi Shehin Malamin ko me zaice a sanar da masoya mabiyan mu a facebook kan wannan lamarin da yake ta yawo a facebook kuma da ruwayoyi daban daban, sai Malam yace min shi tunda yake ma bai taba jin lafiya irin na wannan lokacin da muke ciki ba, yace kuma Da’awa tare da fadin gaskiya ga ko wanene yanzu ma ya fara, yace kuma in ya biyo ta inda ba haske dole ya dauko touch light dinsa ya saka mata battery koda mai cin battery takwas ne, yaci gaba da cewa mutuwa dole ne, in kaji tsoron mutuwa da bakin bindiga koda takwobi kana kan gadonka kana sharar bacci in kwanan ka ya kare zatazo ta dauke ka, Sayyidina Umar R.A. da Sayyida Usman R.A da wuka aka kashe su, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da bakin bindiga aka kashe shi, yace kuma tun lokacin sahabbai ba abin da ya tsaya na Da’awa ana nan ana fafatawa har zuwa lokacin da rai zaiyi halinsa ”inji Shehin Malamin”.
yace kuma sakonsa ga yan uwa shine kowa ya kwantar da hankalinsa yana nan cikin koshin lafiya, mutuwa kuwa da rashin lafiya duka daga wurin Allah suke, in ya aiko su gare shi babu mai iya karewa sai ya same shi, su kuma masu yada jita jita ba gaira babu dalili su dagawa mutane hankali muna addu’an in masu shiryuwa ne Allah ya shirye su, in kuma ba masu shiryuwa bane Allah ka nisan tamu dasu. ya kara da cewa kowa yaji tsoron Allah, ya gyara tsakanin sa da Allah, kuma bai yarda wani yayi raddi kan wai an zage shi ko an masa kage ba, yace amma in wani ya taba Annabi SAW ko sahabban sa Allah ya yarda dasu yace to ya zama wajibi akan mu mu fito mu kare mutuncin su.
Allah sarki Abu Safiyyurrahman, Allah ya tsrae mana shi ya kara daukaka shi ya kuma kare shi daga sharrin masharranta.

(Jibwis Nigeria)

Advertisements

8 Replies to “Wai Malam yayi rantsuwa akan wani mawaki wai yana wuta in kuma ba haka bane Allah ya chanja masa Halitta – Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe. (Secretary General Of Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah Nigeria)”

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s