MAI KIRA ZUWAGA RIKO DA GASKIYA SHINE AKEWA SHARRI !!! MALUMAN SUNNAH MASU WA’AZI DOLENE SU RIKA YIN HAKURI

Maluman Sunnah masu wa’azi dole ne su rika
yin hakuri a kan yabon mai yabo domin kada
yabon ya kai su ga fadawa
cikin gururi, kuma dole su rika yin hakuri a
kan zagin mai zagi ko sharrin mai sharri
domin kada zagin ya sa su yi baya su bar
ayyukan da’awah zuwa ga Sunnah.
Bayan karerayi da da yan’bidi’a suketa
yadawa agari kwanannan akan Shekh kabir
gombe. Mutanen da sukakirani a waya ni
bansan iya kacinsuba badda wadanda suke
samuna gaba da gaba. Abun mamaki Harda
wayanda suke kiran kansu yan Izala. Wato
[Kurdawa]
Lallai sau da dama yan’bidi’a –
mazansu da matansu,maluman su da
jahilansu- cikin ko wane zamani su kan yi
amfani da lafuzan zagi da batanci ba tare da
kafa wata hujja ba, saboda kawai
neman hana mutane fahimtar gaskiya da yin
aiki da ita! Suna iya siffanta musu wa’azi da
cewa: Kafuri ne shi, ko
Munafuki ne shi, ko mai raba kan
al’ummah ne shi, ko mai neman duniya ne shi,
ko mai neman mulki ne shi, da dai sauran
lafuzza masu kama da wadannan. To, amma
irin wannan jinsi na mutane
maluma masu wa’azi ba za su saurare su ba
saboda rashin sauraron nasu shi ne hanyar
Annabi mai tsira da aminci Allah,
Alhafizu Ibnu Katheer ya ce cikin
littafinsa Albidayatu wannihayah 3/55-56:-
((Daga Sa’id Da Jubair da Ikrimah, daga Dan
Abbas ya ce: Shugabannin Quraishawa sun
hadu a Dakin Ka’abah, sannan suka aika wa
Annabi mai tsira da
amincin Allah cewa suna bukatar zama da shi,
nan-da-nan Annabi mai tsira da amincin Allah
ya je ya same su saboda tsammanin da yake
yi na cewa za su musulunta ne, domin shi har
kullum yana son musu alheri ne kuma ba ya
son abin da zai wahalce su.
Da ya zo ya zauna a inda suke sai suka ce da
shi: Ya Muhammad! Lalle, mun aika Maka ne
domin mu yanke uzurinmu gare ka,
wallahi mu ba mu taba ganin wani mutum
daga cikin Larabawa da ya kawo musiba
cikin jama’arsa ba kamar yadda ka kawo
musiba cikin jama’arka ba. Hakika ka zagi
iyayenmu, kuma ka aibanta addininmu,
sannan ka maida masu hankalinmu wawaye,
ka kuma zagi allolinmu, ka raba
kawunan jama’armu. Babu dai wani
mummunan da ya rage wanda ba ka sanya
shi tsakaninmu ba..)).
Yan’uwana Ahlussunnah kadubi abun da
suka fadawa wanda yazowa duniya da shiriya
saboda kawai ya ce: A bi Addinin gaskiya,
kada a karbi umurnin kowa matukar ya saba
wa umurnin Allah Madaukakin Sarki,
da ManzonSa mai tsira da amincin Allah.
Wannan ita ce al’adar karkatattu, sawa’un
mushrukai ne su masu bautar gumaka, ko
kuwa kafurai ne ma’abuta littafi, ko kuwa
munafukai ne, ko kuwa fasikai ne ‘yan bidi’ah
cikin Al’ummar Musulmi.
Saboda haka duk abun da suke fada akan
shekh kabir gombe ko wani malamin sunnah
mai da’awa, basu fada ba sai don kira da yayi
kan arike sunnah ta manzo s.a.w, Abau tawa
Allah atsarin da ya aiko manzosa dashi, Ahada
kai akan gaskiya.
Sai gashi Allah ta’ala ya kunyata munafukai
masu wadannan karerayi Saiga Shekh kabir
gombe a birnin yola yana wa’azi yana kira
zuwaga sunnah.
Ya Allah in masu shiryuwane Allah ka
shiryaddasu in ba masu shiryuwabane Allah
ka mana maganinsu.

Musa H Musa

Advertisements

5 Replies to “MAI KIRA ZUWAGA RIKO DA GASKIYA SHINE AKEWA SHARRI !!! MALUMAN SUNNAH MASU WA’AZI DOLENE SU RIKA YIN HAKURI”

  1. Hello Web Admin, I noticed that your On-Page SEO is is missing a few factors, for one you do not use all three H tags in your post, also I notice that you are not using bold or italics properly in your SEO optimization. On-Page SEO means more now than ever since the new Google update: Panda. No longer are backlinks and simply pinging or sending out a RSS feed the key to getting Google PageRank or Alexa Rankings, You now NEED On-Page SEO. So what is good On-Page SEO?First your keyword must appear in the title.Then it must appear in the URL.You have to optimize your keyword and make sure that it has a nice keyword density of 3-5% in your article with relevant LSI (Latent Semantic Indexing). Then you should spread all H1,H2,H3 tags in your article.Your Keyword should appear in your first paragraph and in the last sentence of the page. You should have relevant usage of Bold and italics of your keyword.There should be one internal link to a page on your blog and you should have one image with an alt tag that has your keyword….wait there’s even more Now what if i told you there was a simple WordPress plugin that does all the On-Page SEO, and automatically for you? That’s right AUTOMATICALLY, just watch this 4minute video for more information at. Seo Plugin

    Like

  2. Assalamu alaikum ‘yan uwa shawarar da xan bamu shine Zambo,Habaici da wulakanta malamai na DARIKA ba shi xai sa su bar wannan muguwar akida ba ta Bidi’a da Shirka,kuma shi zai sa su na ciwa malamanmu na SUNNAH mutunci da zaginsu ta hanyar FACEBOOK wanda har zakaga KIRISTOCI suna gayamana maganganu a matsayinmu na musulmai.Duba shafi mai suna SIFFOFIN ‘YAN BID’A wanda muta nan mu suka bude amma abin takaici ‘yan bid’a sunyi katutu a ciki suna aibata malamanmu.dafatn xamu gyara.Allah ya hada kan al ummar musulmai bisa tafarkin manzon Allah s(.a.w) amiiin.

    Like

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s