Ya kamata ‘yan majalisa su tsige shugaba Jonathan — APC

A Najeriya, Jam’iyar adawa ta APC ta bukaci ‘yan Majalisar dokokin kasar su gaggauta tsige shugaban kasar saboda a cewarta, shugaba Jonathan na kokarin ya wargaza kasar.
Hakan na zuwa ne ya yinda ake ci gaba da tafka muhawara a Najeriyar dangane da wata wasikar da tsohon shugaban kasar Chief Olusegun Obasanjo ya aikewa shugaba Goodluck Jonathan inda ya yi nuni da cewa irin salon mulkin shugaban kasar mai ci yanzu ka iya wargaza kasar.
Ita dai Jam’iyar adawa ta APC ta ce irin bayanan dake fitowa fili game da yadda shugaban kasar Goodluck Jonathan ke tafiyar da mulkin sa, sun nuna cewa abu mafi a’ala ga Najeriyar shine ‘yan Majalisun dokokin kasar su gagggauta tsige shi saboda saba ka’idojin aiki.
Jam’iyyar ta kara da cewa Najeriyar na cikin wani yanayi ne na tsaka mai wuya, ganin irin yadda ake ci gaba da samun rarrabuwar kawuna tsakanin al’umma, matsalar da jam’iyar APCn ta danganta da rashin iya jagoranci.
‘Najeriya na cikin mummunan yanayi’
A cewar Jam’iyyar, matsalar tsaro da cin hanci da rashawa da kuma rashin aikin yi tsakanin matasa wata manuniya ce ga irin yadda shugaba Jonathan ya kasa iya tafiyadda mulkin kasar, inda Jam’iyar ta ce bama ita dake adawa ba, hatta daga cikin gida jam’iyar PDP ana fuskantar wannan zargi.
Laifin cin amanar kasa
Wata sanarwa da ta fito daga Fadar Shugaban Najeriya ta bayyana kiran da Jam’iyyar APC ta yi na cewa a tsige Shugaban Kasa a matsayin laifin cin amanar Kasa.
Sanarwar ta ce gwamnatin Najeriyar zata kama ‘yan adawar da wannan laifi.
Fadar Shugaban Kasar ta kuma ce ba zara zura idanu ba, ‘yan adawar su kawo rudani a cikin Kasar.
Ita ma jam’iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta yi watsi da wannan kira.

Advertisements

One Reply to “Ya kamata ‘yan majalisa su tsige shugaba Jonathan — APC”

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s