SABON KATIN SHEDAR ZAMA ‘DAN KASA ZAI MAYE GURBIN KATIN RIJISTAR ZABE.

Hukumar National Identity Management Commission (NIMC) tace, “Sabon katin shedar ‘yan kasa da ake kan yi a yanzu, zai maye gurbin rijistar masu zabe bayan an yi babban zaben 2015, kamar yadda hukumar kula da yi wa ‘yan kasa sheda (NIMC) ta bayyana.
Mr. Emma Ogungbe daya daga cikin jami’an hukumar shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.
Ya yi bayanin cewa da sabon katin shedar ‘yan kasar, NIMC za ta iya bada bayanai kan duk wadanda suka cancanci yin zabe a duk inda suke a fadin kasar nan.
A cewar Ogungbe katin zai taka muhimmiyar rawa wurin dakile magudin zabe ko masu yin rijistar zaben fiye da daya.
Ya kara da cewa daga lokacin da aka yi nasarar kammala aikin ba wa duk ‘yan kasa katin shedar, babu sauran yin rijistar zabe a gaba, wanda gwamnati za ta samu rarar kudin da ake kashewa don yin aikin.
“Idan NIMC ta kammala yi wa ‘yan kasa sheda, sannan gwamnati ta bukaci ta na son bayanan duk ‘yan Nijeriya za mu dauka mu bada daga kan dan shekaru 18 zuwa sama wadanda kasa za ta sheda zaman su, saboda mun taskance su a cikin na’ura mai kwakwalwa”, in ji Ogungbe.
Baya ga yin aiki a matsayi rijistar masu zabe, har ila yau katin zai yi amfani a matsayin katin cire kudi wato ATM, katin tafiye – tafiye da sauran su.
Dan haka kada ka tsaya kallon Ruwa Kwado ya Maka Kafa,
Garzaya Maza Ka Nemi Inda Ofishin NATIONAL IDENTITY MANAGEMENT COMMISSION (NIMC) yake a Fadin Jihar ku.

Ka Tafi da Daya Daga Cikin Wadannan;
-Takardan Shaidan Haihuwa.
-Takardan Shaidar gama Primary.
-Takardan Shaidar Zama Dan Gari (Indigene Letter)
-Tsohon Katin Dan Kasa.
-Nat. Driving License.
-International Passport.
-Katin Shaidar Aiki. (Identity Card)
Ana Bukatar ka tafi da daya daga cikin abubuwan da muka lissafan.

Inda Hali ka Cika Form Dinka a Gida ko Çafe kafin Kaje Office din ta wannan Adireshin!
http://216.87.173.150/penrol
Koh
http://www.ninenrol.gov.ng
Sai kayi printing ka tafi da shi a hannunka, in ka isa babu ruwanka da jiran dogon layin da mutane suke bi, Kawai zasu dauki hotonka ne da hoton yatsunka su sallameka.

Akwai Bukatar Mu dauki wannan abin da muhimmanci, domin duk wata makarkashiya da za’a mana ana iya yi mana ta wannan hanyar.
An jima da farawa amma anki wayar mana da kai akan ya za’ayi.
Allah ya bamu sa’a.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s