Za’a fara gwajin motoci marasa matuka a karo na farko a UK bayanda gwamnati ta bayar da fam miliyan daya da rabi.

Motocin, masu tafiyar kilomita 19 a sa’a daya, za su dauki mutane ne a garin Milton Keynes a wadansu hanyoyi da aka kebance musu.
Nan da 2015 za’a gwada motocin guda 20 wadanda ke bukatar matuki, amma dai ana sa ran zuwa 2017 za’a samar da motoci marasa matuka guda 100, a cewar hukumar kasuwanci da kirkire-kirkire.
A yanzu haka dai akwai irin wadannan motocin da ke aiki a filin jiragen sama na Heathrow.
Sabuwar fasaha
Gwamnatin Britaniya dai ta ware fam miliyan 75 domin tallafawa kamfanoni samar da injina marasa shan mai da yawa, shirin da tace zai baiwa kasar damar rike kambunta na jagaba a fasahar kera injina tare kuma da kare ayyukan mutane dubu 30.
Ana iya hawa motocin marasa matuka masu amfani da wutar lantarki, da ke daukar fasinja biyu ne ta hanyar amfani da wayar komai-da-ruwanka.
Matafiya cikin motocin marasa matuka dai za su iya shiga intanet, su duba sakonnin i-mel, su karanta jarida, su kuma buga wasanni a cikin motar. Kawo yanzu dai ba’a bayyana farashin bulaguro a cikin motar ba.
A cewar gwamnatin UK, idan shirin ya yi nasara za’a yi amfani da shi a sauran birane da garuruwa na kasar.
Kamfanin aikin injiniya na Arup da jami’o’in Cambridge da Oxford na daga cikin wadanda suke aikin samar da motocin.
A Amurka dai, an baiwa kamfanin Google lasisin gwajin motocin, in da ya ce bayan gwajin kilomita kusan dubu 500, babu wani hatsari da aka samu da motocin.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s