Microsoft ya fito da Windows 8.1

Kamfanin manhaja na Microsoft ya fitar da ingantacciyar masarrafarsa mashahuriya ta Windows 8.1.
Masarrafar ta yi kokarin inganta wasu abubuwan da aka yi suka a kansu, a masarrafar da ta gaba ce ta Windows 8.
Ga misali sabuwar manhajar ta maido da abin da ake latsawa domin bude kwamfuta, kuma ta kan bude kwamfutar ta hanyar da aka saba.
Kaddamar da masarrafar ta zo ne a lokacin da Microsoft ke neman sabon shugaba, bugu da kari ga rashin ciniki da kwamfutocinsa suka dauki dogon lokaci suna fama da shi.
Cike gibi
Windows 8 ya yi kokarin cike gibin da ake da shi tsakanin na’urorin da ake latsa su, da kwamfutocin tafi da gidanka da wayoyin komai da ruwanka da kwamfutar tafi da gidanka da ta kan teburi.
Saboda haka an yi ma masarrafar fuska ta yadda za a iya latsa wa ko a shafa, idan ana son manhajoji su bayyana.
Amma mutane da dama ba sa jin dadin yadda fuskar kwamfutar take, domin ba kamar yadda suka saba amfani da kwamfuta ba ce.
Massarrafar da aka inganta ta Windows 8.1 kyauta ake sauko da ita ga wadanda ke da Windows 8, amma masu amfani da Windows 7 sai sun biya wasu ‘yan kudi tukuna.

Via: https://m.facebook.com/nazeeerdanjagale

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s