MI YASA KAKE FACEBOOK….???

Allah ya qaddara mana zuwan shafin sada zumunta a wannan zamani da muke ciki, yadda za kaga mutum na hulda da dubban abokai na kusa dana nesa maza da mata. Yara da manya, wadanda ka sani da wadanda baka sani ba. Wannan yasa bakin abokai da sabbin al’adu da dabi’u ke ta kwararo mana don tasirin abokan hulda na facebook.
Ta hannun dama ana samun dacewa da mutanen kirki masu halin nagarta da kishin addini, a qulla alaqa sosai, a so juna don Allah ayi ta nishadi cikin bin Allah da kare sunnar Annabi (saw), da yaqar miyagun Aqidu don tabbabtar da cigaban addini. Samun wannan abin sha’awa ne da burgewa.
Haka nan ta hannun haggu ana samun miyagun abokai batattu masu batarwa su mamaye zukatan jama’a su gurbata addini da al’adunsu suna ji suna gani.
Duk abinda kowa keyi Allah yana gani kuma yana ji, don haka mu nisanci sabawa Allah ta hanyar abotar facebook.
Wannan shafin zumunta na facebook ya jawo alheri mai yawa da sharri mai yawa a cikin mu.
Da yawa wassu yaudara da damfara ne ya kai su yin fcbk, wassu kuma anan ake koyon badala da fasikanci musamman matasa. Haka nan ana samun masu shiga kungiyoyin fasikai, ‘yan luwadi, mazinata, barayi da sauran su.
In muka duba wani bangare kuma da wannan shafi ana iya dawo da zumunta har a karfafa alaqa ta kasuwanci, aure, da sauran su.
Sahihan bayanai sun tabbatar da cewa ta fcbk ne wassu ke siyasa, ko saye da sayarwa, da fara neman aure, da sauran su. Abin damuwa shi ne yadda zaka ji labari maras dadi duk sai ace maka fcbk ne ya jawo.
Nasiha ta garemu a yau shi ne pls kowa ya duba irin mu’amalar da yake yi da wani a fcbk, mu tsaya sosai mu hada kai da juna muyi zumunci akan alheri. Mu taimaki juna da nasiha da shiryarwa, cikin kur’ani Da sunnah.
Mu guji kusantan miyagun mutane masu yawan aiyukan zunubi a fcbk, kuma mu kusanci wuraren alheri.
Tabbas kowa abinda ya shuka anan duniya shi zai girba a lahira. Pls kowa ya tambayi kansa mi yasa ka shiga shafin fcbk..???

Via: Shaykh Aliyu Said Gamawa (Hafizahullah)

Allah ya saka da alkhairi….
Anan nake son nayi amfani da wannan damar domin nayi wani dan tanbihi, doriya akan abinda malam (Allah yasaaka da Alkhairi) ya fada! Hakika yah ku ‘Yan uwa, mu sani wadanda suka kirkiri wannan fasahar, ba musulmai bane, sannan ba manufarsu ba ne su taimakawa musulmai da musulunci ya ciga ba da yaduwa, a a, zan iya cewa sunyi ne domin su cu cemu su bata mana lokaci, su shagaltar da mu ga barin neman gwaggwabar lada da lokacin mu, su shagaltar damu kamar yadda su, suka shagala!a saboda haka, bai kamata mubi wannan tarkon nasu ba, sai mu kuma mu juya shi yazamar mana wajen yada da awa, da nasiha, da tunatarwa, ga yan uwanmu musulmai. abin nufi mu chanja asalin manufar FCBK din ya zamana muna amfani da shi domin yada kalmar Allah da Sunnar Annabi (SAW) a bayan kasa. Yah kai dan uwa/Yar uwa a musulunci, ina yiwa kaina da ku nasiha, mu sani duk abinda kwakwalwa ta kirkiro, zuciya ta shirya, harshe ya furta, hannuwa suka rubuta wallahi ababan Tambaya ne, a ranar da ba a chanja amsa, ranar da ba a alfarma, ranar da ba a danasani, ranar da ba wani sai Allah mahalicci Maigirma!. Allah ya sa mu amfana da abin da Mallam ya fada kar damu akai! Ma assalam. Mu wuni lafia Allah ya bamu albarkan wannan wunin

Via: Abdallah Abdulhameed

Advertisements

3 Replies to “MI YASA KAKE FACEBOOK….???”

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s