MU GUJI KAZAMIYAR RAYUWA DA DABI’A MAI HALAKARWA A DUNIYA DA LAHIRA

‘Yan uwa mun shiga wani zamani mai juyawa yana canzawa daga nasara zuwa hasara, wassu kuwa daga bata zuwa shiriya, ko daga zaqi zuwa daci..
Dan adam ba dabba bane, kazamta ba tsabta bace, aikin zunubi baya taba zama lada ko shiriya har sai an tuba an koma ga Allah an nemi tsira da rahmar Allah.
Tabbas komi da kowa ikon gudanar da rayuwar sa na hannun Allah koda waye shi.
Naji damuwa da tausayin jin yadda kazamiyardabi’ar dabbanci ta Luwadi da Madigo ya yawaita tsakanin al’ummar mu ta yau musamman matasa da wassu masu dukiya.
Mafi yawan su har kungiya ko kawance sukeyi da lalata juna, ana bin jinsi ba tsoron gamuwa da Allah. Ana bayyana komi a fili ba tsoro ko kunya.
To mu sani duk ma suyi don tsafi, da masu yi don bin umarnin bokaye, da masu biyan bukatar sha’awar su ta wannan kazamiyar hanya to basu da makoma a duniya da lahira sai halaka da cutar da kansu da gadar da wulakanci ga rayuwar su da zuriyar su.
Mu tuna tarihi a baya Allah ya aiko da hani akan wadannan mummunar hanya, kuma an kifar da masuyin wannan aiki da halakar dasu. Sannan hanya ce ta kaskantattu da yadacuta a junan su.
Ga mugun aikin yana da wuyan bari, kuma yana busar da zuciya. Kuma ana samun gafalada yin nesa ga kwadayin rahamar Allah ga mai wannan aiki. Munafurci da yaudarar juna na yawaita tsakanin masu wannan aiki da kyamar juna a rayuwar su.
Tabbas ba alheri cikin wannan aiki sai nadama da nisa daga rahmar Allah. Kuma anan duniya a fada ganin kyama da kaskanci cikin dukkan al’amurran rayuwa.
Mu tuba ga Allah, muyi kwadayin rahamar sa, mu ji tsoron Allah yayi fushi damu, mu godewa ni’imar rayuwa da Allah yayi mana.
Mai wannan aiki ya ji tsoron kada ya zamo masa ajali, ko aikin sa na karshe yayin komawar sa ga Allah yana cikin mummunan aiki irin wannan aiki.
Zai yiwu rudin abokai ne ya jefa ka wannan aiki, ko son duniya na kwadayin dukiya, ko neman shugabanci, ko bin umarnin masihirta bokaye’ to duk ba zai zamo alheri gareka a duniya da lahira.
Daga Sheikh Aliyu Sa’id Gamawa.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s