ABUBUWAN DA AZUMI YAKE KARANTARWA.

Makarantar azumi tana tarbiyyantarwa kan karfin niyya da gaskiyar niyya. Wadannan su ne ke karya turakun son zuciya su mayar da igiyoyin sharri. Duk wani karfi ko tsari zai yi wuya ga mumini daga mafitar rana zuwa mafadarta yana cin abinci ko abin sha na wani lokaci. Za ka gan shi yana rike da akalar rayuwarsa yana hana ta fadawa ga sha’awoyi ko wasu abubuwa na son zuciya. Kai yana iya cewa zuciyarsa Naƙi.
Me ya fi dadi a ce ta kasance cikin neman yardar Allah. Ba ta jima’i da rana ba ta fasiƙanci. Kuma da jahili zai bata mata ya nemi tayarda hankalinta, sai ya yi linzami ga fisgar sharri da fadinsa: “Ni mai azumi ne!”

Azumi na gaskiya yana tsarkake zuciya daga miyagun ƙullace-ƙullace da zunubai da sharruka. Yana ƙange harsuna daga furta lagawu (maganganun banza) da hana ido ganin haram.
Amma daga cikin masu azumi akwai mai azumin da ba ya da komai sai yunwa da kishin ruwa. Eh mana, domin mutumin da ke barin abinci, amma ya ci naman ’yan uwansa da giba, yana kamewa daga shan abin sha, amma bai kamewa daga ƙarya da algushu da zaluntar mutane, yunwa da ƙishi kawai yake sha.
Azumi na gaskiya yana sa Musulmi ya zama mai fadaddar zuciya da harshe mai laushi, ya zamo mafi gudu daga husuma da sharri, idan aka yi masa laifi ya hakura, in aka munana masa ya yi hakuri. “Masu hakuri kawai ake cika wa ijararsu, ba da wani lissafi ba.” (Ƙ:39:10).
Daga cikin albarka wannan wata mai girma, akwai falalar ayyukan kirki.
Daga ciki akwai tsayuwar dare, hakika Manzon Allah (SAW) ya kasance yana kwadaitarwa kan Tsayuwar Ramadan yana cewa: “Wanda ya yi Tsayuwar Ramadan yana mai imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa.”
Sai yin sadaka, saboda Annabi (SAW) ya fi dukkan mutane yin kyauta, kuma ya fi yin kyautar da sadaka a cikin Ramadan lokacin da yake ganawa da Jibrilu kamar yadda Buhari da Muslim suka ruwaito.
Kuma an so a gaggauta buda-baki da yin addu’a yayyin shan ruwa. hakika Tirmizi ya ruwaito cewa: “Lallai Annabi (SAW) ya ce: “Mutum ukku ba a mayar musu da addu’arsu. i.e;
i) Shugaba adali
ii)mai azumi lokacin da yake buda-baki
iii) wanda aka zalunta.”

Ya bayin Allah! Ku yi salati ga Manzon shiriya. Hakika Allah Ya umarce ku da hakan a cikin LittafinSa: “Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.”
Ya Ubangiji! Ka kara tsira da aminci a bisa bawanKa, kuma ManzonKa Muhammad da alayensa. Kuma Ka yarda da halifofin nan hudu masu shiryarwa.
Ameeen.

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s