SAKO NA MUSAMMAN DAGA ASH-SHEIKH ABDULLAHI BALALAU (Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah Ta Kasa

Da sunan Allah mai Rahama mai Jinqai.
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, muna gode masa, kuma muna neman taimakonSa, da gafarar sa. Muna neman tsarinsa daga dukkan sharri.
Ina so inyi amfani da wannan lokaci mai albarka domin in gabatar da gaisuwa, tunatarwa da addu’a ga dukkan Musulmin wannan kasa mai albarka kuma a wannan wata na Ramadan mai tarin albarka da falala.
Allah madaukakin sarki yana cewa:”Watan Ramadan wanda a cikinsa aka saukar da Al-Qur’ani, shiriya ga mutane, kuma bayyanannar shaida ta shiriya da….” [Qur’an:185].
Wannan wata na Ramadan wata ne mai daraja, falala da muhimmanchi a Musulunchi. Shine watan Al-Qur’ani, watan azumi, watan albarka, alfarma, gafara, falala da fa’idodi masu yawan gaske. A takaice, shine watan da yafi ko wane wata muhimmanchi da fa’idodi cikin watanni goma sha biyu na shekara.
A cikin wannan wata ne Allah ya saukar da Al-Qur’ani, kuma a cikinsa ne daren “Lailatul Qadri” yake fadowa, wanda ya fi watanni dubu falala.
Kuma watan Ramadan wata ne da musulmai ke zage damtse wurin tausayi, kyautatawa, kame kai daga barin alfahsha, haquri, sadaqa da ‘yan uwantaka. Cikin wannan wata ne ake samun dukkan alkhairi. Wannan wata babban bako ne da duk musulmi na kwarai ke kosawa da marhaba da zuwansa. A wurin bayin Allah na gari kuwa, watannan dama ne na ‘kara kusantar Allah. Kuma ga masu son shiriya, wannan wata dama ne na barin alfahsha, al-kaba’ir, da munanan ayyuka domin komawa ga Allah. Don a wannan watan duka shai’danu an ‘daure su kuma an kulle su.

Saboda haka, ina so in tunatar da shugabanni da wadanda ake shugabanta na wannan kasa da suyiamfani da wannan wata mai albarka don kara tausayi, gaskiya, amana, adalchi da tuhuman kawunanmu kan ayyukanmu.
Sannan kuma har yanzu ina amfani da wannan dama domin jawo hankalinmu da mu guji ta’addanchi, ha’inchi, chin zali, rashin ‘da’a, chin amana, fasadi, alfahsha, fadace-fadace, tada hamkula, izgili, qazafi, sharri da chin hanchi da rashawa!
Ina mai horon dukkan musulmi ba tare da la’akari da matsayi, kudi, kabila, gari, ko jinsi ba, da mu dauki wannan watan na Ramadan a matsayin bako da ke zuwa sau daya a shekara. Wata ne na ‘yanchi, gafara, rahama, tuba da zage damtse wurin bautan Allah.
Ina kira a garemu da mu tuba, tuba na gaskiya ga Allah, kuma mu inganta dangantakarmu da Allah ta hanyar yin azumi, sallolin nafila, karatun Qur’ani, sadaka, kyauta, ‘da’a, da yawaita addu’o’i. Saboda an bamu wannan wata ne domin mu inganta imaninmu da kara tsoron Allah.
Allah yana cewa a cikin Suratil Bakara, aya ta 183:”Ya ku wadan da kuka yi imani, an wajabta(sanya) muku azumi kamar yadda aka wajabta wa wadanda suka gabaceku domin ko zaku samu tausayi da tsoron Allah.” daga ‘karshe, a cikin wannan wata mai albarka, kasarmu Nigeria tana bukatar addu’o’inmu managarta daga dukkan bakunanmu. Domin Allah ya zaunar damu lafiya, kuma ya karemu daga dukkan sharrin masu sharri!
Ina addu’a Allah ya zaunar damu lafiya, ya yafe mana zunubanmu, ya kyautata zamantakewarmu, kuma ya karemu daga fitintinun da kasarmu ke ciki wadanda suka hadada rashin tsaro, rashin adalchi, rashin amana, chin hanchi da rashawa da sauransu!
Ameen Summa Ameen!!!

Wannan Sako ne na Musamman daga Sheikh Abdullahi Bala Lau,
Shugaban Kungiyar Jama’atu IzalatilBidi’ah Wa Iqamatis Sunnah ta Kasar Najeriya.
RAMADHAN KAREEYM!!!

Advertisements

2 Replies to “SAKO NA MUSAMMAN DAGA ASH-SHEIKH ABDULLAHI BALALAU (Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah Ta Kasa”

  1. Please take part in this & forward it to all Muslims and let everyone take part in the Dua.
    Yaa Allah don’t take my soul away until you are happy with me:Ya Allah give me a death of a shaheed. Ya Allah grant me death while I’m in sujuud. Ya Allah let the last words of my life be the Shahadah. Ya Allah If I die in my sleep let My heart beat the Zikr of Allah. Oh Al
    the guider of the lost soul forgive the entire Muslim Ummah! Ya Allah Forgive my Parents, my Family, my Muslim Friends. Ameen Thumma Ameen. Send this Dua to all Muslims, without failing to say Ameen.The fire in Jahanam will not touch the person who recites “Allahumma Ajirni Minan Naar” 7x after fajr & maghrib. If u choose to forward this message, it will be a Sadqatul-Jaariya 4 u and me

    Like

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s