Fatawa A Kan Qunuti Domin ‘Yan Uwanmu Musulmin Yobe da Borno

BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM
Assalamu alaikum ‘yan uwa musulmi Dukkanmu muna sane da halin da ‘yan uwanmu musulmi suke ciki a jihohin Borno da Yobe a cikin ‘yan kwanakin nan bayan kafa dokar ta bacin da gwamnatin tarayya ta yi a jihohinsu.
An yanke hanyoyin sadarwa tsakaninsu da sauran jama’a, kuma rahotannin da kafafe masu zaman kansu ke bayarwa sun nuna suna cikin halin damuwa qwarai, abinda ya wajabta mana taimaka ma su da addu’a.
Kasancewar sunnah ta zo da yin addu’ar qunuti a irin wannan hali muka ga yadace mu yi wa ‘yan uwa bayani a kan wannan addu’a da hukunce-hukunce­nta daidai da sunnah don mu yi aiki da ita saboda taimakon ‘yan uwanmu.
1. Wannan addu’a ana kiran ta “Qunutun Nawazil” kuma ana yin ta a lokacin da wasu musibbu suka sauka ga wasu musulmi. Ana kuma yin ta ne a dukkan sallolin farilla.
Ya tabbata daga hadisin Anas bin Malik (RA) cewa Annabi (SAW) ya yi wata daya yana qunuti yana la’antar qabilun Ri’il da Zakwan da Usayya da Banu Lihyan saboda sun yaudare shi; sun kashe sahabbansa saba’in mahardatan Alqur’ani.
2. Qunutin ana yin sa ne a raka’ar qarshe bayan tasowa daga ruku’i kamar yadda sayyidina Abu Huraira (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) ya yi a lokacin da kafiran Makka suka riqe wasu musulmi masu rauni suka hana su yin hijra.
3. Wanda yake sallah shi kadai zai iya yin qunuti. Haka shi ma liman zai yi shi a bayyane – a dukkan salloli – kuma masu bin sa suna cewa “Amin” kamar yadda Ibnu Abbas (RA) yaruwaito. Abu Dawud ya ruwaito shi kuma Nawawi da Ibnul Qayyim sun inganta shi.
4. Ba a tsawaita qunutin kamar yadda sayyidina Anas (RA) ya fada. Kuma ba a yin wasu addu’oi sai addu’ar da dalilinta ya kama, sannan ba a rufe shi da salati irin yadda ake rufe qunutin witri kamar yadda wasu sahabbai ke yi.
5. Ana ci gaba da yin qunutin har Allah ya kawar da matsalar da ta sa ake yin sa. Zadul Ma’ad na Ibnul Qayyim (1/272).
6. Hikimar yin sa bayan ruku’i, ba a cikin sajada ba ita ce, samun cewa “amin” daga masu bin liman sallah. Fathul bari (2/570).
7. Ana daga hannuwa a cikin wannan qunutin kamar yadda Baihaqi ya ruwaito a cikin Sunan(2/212).
8. Ana iya yin amfani da addu’ar manzon Allah(SAW) sai a shigar da buqatar da ake qunuti a kan ta. Misali, ana iya cewa:
“اللهم أنج إخواننا المسلمين في بورنو، اللهمأنج إخواننا المسلمين في يوبي، اللهم انصرهم ، اللهم اشدد وطأتك على من ظلمهم وقاتلهم، ومنشايعهم وأعانهم يا قوي يا عزيز”.
Ko kuma ayi amfani da ta sayyidina Umar (RA) lokacin da yaqi ya tsananta tsakanin sa da Nasara. Sunan Al-Baihaqi (2/210) da Irwa’ul Galil na Albani (2/170).
“اللهم إنا نستعينك ونؤمن بك، ونتوكل عليك، ونثني عليك الخير، ولا نكفرك، اللهم إياك نعبد، ولك نصلي ونسجد، وإليك نسعى ونحفد، نرجورحمتك ونخشى عذابك، إن عذابك الجدَّ بالكفار مُلحق، اللهم عذِّب انصر إخواننا المسلمين في برنو ويوبي، اللهم نج المسلمين وفُكّ أسرهم، وتولّ أمرهم، وارحم حوتاهم، وكن لهم عونا ونصيرا في أراملهم وأيتامهم يا ذا الجلال والإكرام”
9. Ba a shafa fuska bayan gama qunuti domin bai zo a Sunnah ba kamar yadda Imamun Nawawi ya fada. Al-Majmu’u na Nawawi (3/490).
10. Ba a yin sa a sallar jum’ah saboda shi ma bai tabbata ba a cikin Sunnah. Kuma wasu daga cikin sahabbai sun hana. Musannaf na Abdurrazzaq (3/194) da Musannaf na Ibn Abi Shaibah (2/46).
11. Idan liman bai yi qunuti ba Mamu ba zai yiba saboda Annabi (SAW) ya ce, “Kada ku sava ma limamanku”. Majmu’u Fatawa Ibn Taimiyya(23/115-116)

Allah ya sa mu dace. Allah ya kawar da fitina daga qasarmu da sauran qasashen musulmi. Allah ya hada kan musulmi a kan gaskiya.
Wassalamu Alaikum
Warahmatullah

Via Dr Mansur Sakkwato

Advertisements

What can you say about this post?

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s