SHK YAKUBU MUSA KATSINA 2015 TAFSEER.

Domin Sauraron 2015 Tafseer daga babban Masallacin JIBWIS dake Kofar Kaura Katsina (Kandahar) daga bakin Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina (SAUTUS SUNNAH) Tare da Alaramma Abubakar Adam Katsina, da kuma Ustaz Saifuddeen Yakubu Musa. dannan wannan link na kasa don ka bude folder din ka sauke wanda kake so a wayarka. kiwi6.com/folders/wcej8nmrrq

KADA A MANTA AYI LIKE NA PAGE NAMU: fb.com/JibwisKtn

SANNAN AYI JOIN NA GROUP NAMU: fb.com/groups/jibwisktn

An gano Qur’anin da yafi dadewa a duniya.

Binciken ya nuna cewa wani masanin tarihi ne ya kai takardun Al-Kur’anin Jami’ar Birmingham.
Fb.me/nmdblogs
Masu bincike a Jami’ar Birmingham da ke Biritaniya sun ce sun gano wasu daga cikin takardun Al-Kur’anin da mai yiwuwa suka fi tsufa a duniya.
Masu binciken sun ce wani nazarin kimiyya da suka yi a kan takardun sun nuna cewa an wallafa su ne a karni na bakwai don haka kusan shekarun su 1,370 a duniya.
Sun kara da cewa mai yiwuwa mutumin da ya rubuta Al-Kur’anin ya taba haduwa da Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) ko kuwa ya taba jin sa yana wa’azi.
Binciken ya nuna cewa wani masanin tarihi dan kasar Iraki, Alphonse Mingana ne ya kai takardun Al-Kur’anin Jami’ar ta Birmingham a shekarun 1920.
Takardun Al-Kur’anin sun kwashe kusan shekaru 100 a dakin karatun Jami’ar ba tare da an kula da su ba.

Wani mai nazari a kan irin wadannan takardu a dakunan karatun Biritaniya, Dr Muhammad Isa Waley, ya gano takardun Al-Kur’anin “zai farantawa Musulmai rai”.
Daraktar Jami’ar da ke kula da tsofaffin takardu, Susan Worrall, ta ce “mun yi matukar farin ciki da muka gano cewa muna ajiye da takardun Al-Kur’ani mafi dadewa a duniya”.
Kazalika, binciken ya gano cewa an rubuta Al-Kur’anin ne a kan fatun dabbobi.
Farfesa David Thomas da ke nazari kan addinan Musulinci da Kiristanci a Jami’ar ya ce gano Al-kur’anin “zai iya taimakawa domin gano shekarun da aka karbi Musulinci a duniya”.
Ya kara da cewa “Musulinci ya nuna cewa Annabi Muhammad (SAW) ya karbi wahayi tsakanin shekarar 610 da 632, lokacin da ya yi wafati.”

HOMOSEXUALITY!!!

Whether u are a Muslim or Christian, male or female, young or old, as far as u have an atom of faith in u, be ready to defend Nigeria and Africa at large from the ever destructive act of homosexual. Satan and his allies cannot defeat a single faithful let alone Nigerian or African. They have made a plan to infect Nigeria with it and u shall not have single excuse before God for not rejecting it AT ALL COST. Be one of ambassadors of God by sending this message through Whatsapp, Facebook, 2go, twitter etc. As much as u can.

Jibwis Caller Tunez

Ga Masu Bukatar In An Kira wayar su maimakon aji wani abu daban, sai aji muryar manyan Malamanmu da Alarammomi. Yi Maza ka shiga Akwatin Tura Sako na wayar ka (Text Message), sai ka tura lambobin da zamu rubuta maka kamar Haka: 1- Sheikh Abubakar Gummi! MTN- 01886 to 4100 2- Sheikh Bala Lau! MTN- 718382 to 4100 AIRTEL- 0300942 to 791 ETISALAT- 820954 to 251 3- Sheikh Kabiru Gombe! MTN- 718383 to 4100 AIRTEL- 0300941 to 791 ETISALAT- 820967 to 251 4- Alaramma Ahmad Sulaiman! MTN- 011654 to 4100 MTN- 011655 to 4100 MTN- 011656 to 4100 5- Alaramma Nasiru Gwandu! MTN- 018772 to 4100 MTN- 018773 to 4100 MTN- 018776 to 4100

An bullo da hanyar rufe Facebook na matattu.

Facebook ya dade yana neman hanyoyin
taimakawa mutane tunawa da ‘yan uwansu da
suka mutu
Shafin sada zumunta na Facebook ya bullo da wata
hanya ta bai wa mutane damar rufe shafukansu har
abada idan sun mutu.
In kuma mutane suna so, za su iya zaban aboki ko
dan uwa ya ci gaba da tafiyar da wasu abubuwa a
shafukan nasu bayan mutuwar su.
Wadannan sababbin abubuwa da shafin Facebook
ya bullo da su, suna daga cikin abubuwan da
mutane suka fi nuna bukatarsu daga shafin na
Facebook.
Sai dai a yanzu, masu mu’amala da shafin Facebook
a Amurka ne kawai zasu iya amfani da sabbin
hanyoyin da shafin ya bullo da su.
Mahukuntan Facebook suka ce sababbin tsare
tsaren da aka bullo da su zasu sa ‘yan uwa da
abokan arziki su rika tunawa da wadanda suka
mutu.
Idan mutun ya amince wani ya ci gaba da tafiyar da
shafinsa na Facebook, za a iya yin rubutu a shafin
nasa da karbar sabbin abokai da sauya babban
hoton shafin da sauransu bayan ya mutu.
Shafin Facebook ya dade yana neman hanyoyin
taimakawa iyalai tunawa da ‘yan uwansu, saboda
bukatar shiga shafukan mamata da manyan mutane
suka yi ta nuna wa.

DORA DAMA AKAN HAGU CIKIN SALLAH SHI NE SUNNAH, SAKIN HANNAYE CIKIN SALLA SABANIN SUNNAH NE

Imamush Shaukaanii ya ce cikin littafinsa Nailul
Autaar 2/205: ((Hadithan dora dama a kan hagu
ishrin ne suka zo daga Annabi mai tsira da amincin
Allah ta hanyar mutum goma sha takwas, tsakanin
Sahabi da Tabi’i)).
Ga wasu daga cikin hadithan da Imamush Shaukaanii
ya yi maganarsu:-
1- Imamu Muslim ya ruwaito hadthi na 401 cewa:
Annabi mai tsira da amincin Allah: ((Ya kasance yana
dora hannun damansa a kan hagunsa)).
2- Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 740 da
Imam Malik cikin Muwattaa hadithi na 546 cewa
Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yana
umurtan sahabbansa da dora dama a kan hagu:
((Mutane sun kasance ana umurtan su da cewa:
mutum ya dora damansa a kan zira’insa na hagu a
cikin Salla)).
3- Imamut Tabaraanii ya ruwaito cikin Almu’ujamul
Kabiir hadithi na 11,323, da Imamud Daara Qudnii
cikin Babun Fi Akhzish Shimaal Bil Yamiin hadithi na
3, da Imam Ibnu Hibbaan dadithi na 1,770, da Imam
Sulaimaan Ibnu Dawud Attayaalisii cikin Musnad
hadithi na 2,776 cewa Annabi mai tsira da amincin
Allah ya kasance yana cewa: ((Mu taron Annabawa
an umurce mu da gauggauta buda-baki, da jinkirta
sahur, da kuma mu dora hannayenmu na dama a kan
hannayenmu na hagu)). Albaanii ya inganta hadithin
cikin Sahihul Jami’is Sagiir 1/454.
4- Imam Ahmad ya ruwaito hadithi na 15,090, da
Imam Abu Dawud Hadiyhi na 755, da isnadi sahihi
cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ((Ya
wuce wani mutum yana salla amma ya dora
hannunsa na hagu a kan na dama, sai ya balle
hannun ya dora daman a kan hagun)).
5- Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 727, da
Imam Nasa’ii hadithi na 963, da Imam Ibnu
Khuzaimah hadithi na 480 da isnadi sahihi cewa
Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ((Ya kasance
yana dora dama a kan bayan tafinsa na hagu, da
kuma wuyan hannu, da dantse)).
6- Imama Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 759, da
Imam Ibnu Khuzaimah hadithi na 479 cewa Annabi
mai tsira da amincin Allah ((Ya kasance yana sanya
hannun damansa a kan hagunsa, sannan sai ya hada
tsakaninsu a kan kirjinsa alhalin yana cikin salla)).
TAMBAYOYI TARE DA AMSOSHINSU:
(1) Idan wani ya ce: Amma kuma ai Imamut Tabarii
ya ruwaito cikin littafinsa Almuujamul Kabiir hadithi
na 16,563, daga Sahabi Mu’azu Dan Jabal ya ce:-
(( ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺻﻼﺗﻪ ﺭﻓﻊ
ﻳﺪﻳﻪ ﻗﺒﺎﻟﺔ ﺃﺫﻧﻴﻪ، ﻓﺈﺫﺍ ﻛﺒﺮ ﺍﺭﺳﻠﻬﻤﺎ، ﺛﻢ ﺳﻜﺖ، ﻭﺭﺑﻤﺎ ﻳﻀﻊ
ﻳﻤﻴﻨﻪ ﻋﻠﻰ ﻳﺴﺎﺭﻩ )).
Ma’ana: ((Annabi mai tsira da amincin Allah ya
kasance idan yana cikin sallarsa sai ya daga hannu
daura da kunnensa, idan ya yi kabbara sai ya sake
su, sai kuma ya yi shiru, wani lokaci ma nakan gan
shi yana dora damansa a kan hagunsa)). Wannan
hadithi ai shi ne hujjar sake hannu!!
Sai a ce da shi: Da farko dai ya kamata ka san cewa
wannan hadithi maudhuu’i ne, watau hadithi ne da
cikin isnadinsa akwai makaryaci kazzaabi wannan
kuwa shi ne: Khasiib Bin Jahdar, ya zo cikin littafin
Miizaanu Litidaal 1/653 kamar haka:-
(( ﺍﻟﺨﺼﻴﺐ ﺑﻦ ﺟﺤﺪﺭ: ﻋﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺩﻳﻨﺎﺭ، ﻭﺃﺑﻲ ﺻﺎﻟﺢ
ﺍﻟﺴﻤﺎﻥ، ﻛﺬﺑﻪ ﺷﻌﺒﺔ ﻭﺍﻟﻘﻄﺎﻥ ﻭﺍﺑﻦ ﻣﻌﻴﻦ. ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺣﻤﺪ : ﻻ
ﻳﻜﺘﺐ ﺣﺪﻳﺜﻪ . ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ: ﻛﺬﺍﺏ ﺍﺳﺘﻌﺪﻯ ﻋﻠﻴﻪ ﺷﻌﺒﺔ )).
Ma’ana: ((Khasiib Bin Jahdar: daga Amr Bin Diinaar,
da Abu Salihis Sammaan: Shu’ubah, da Qattaan, da
Ibnu Ma’iin sun karyata shi. Ahmad ya ce: Ba a
rubuta hadithinsa. Bukharii ya ce: Makaryaci ne,
Shu’ubah ya yi bayanin karyarsa))
Na biyu: Da za a kaddara cewa hadithin ingantacce
ne, to da sai a fassara shi da cewa: yana nufin bayan
Annabi ya daga hannayensa daura da kunnuwansa
lokacin kabbarar harama, ya kan sake hannayen nasa
ne zuwa kirjinsa, dole a yi irin wannan fassarar
saboda hadithin ya dace da sauran hadithai
ingantattu cikin babin.
Babban masanin ilmin hadithi Alhaafiz Ibnu Hajar ya
ce cikin littafinsa: Attalkhiisul Habiir 1/554:-
(( ﺗﻨﺒﻴﻪ : ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻐﺰﺍﻟﻲ : ﺳﻤﻌﺖ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻤﺤﺪﺛﻴﻦ ﻳﻘﻮﻝ : ﻫﺬﺍ
ﺍﻟﺨﺒﺮ ﺍﻧﻤﺎ ﻭﺭﺩ ﺑﺎﻧﻪ ﻳﺮﺳﻞ ﻳﺪﻳﻪ ﺍﻟﻰ ﺻﺪﺭﻩ، ﻻ ﺍﻧﻪ ﻳﺮﺳﻠﻬﻤﺎ ﺛﻢ
ﻳﺴﺘﺄﻧﻒ ﺭﻓﻌﻬﻤﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺼﺪﺭ . ﺣﻜﺎﻩ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺼﻼﺡ ﻓﻲ ﻣﺸﻜﻞ
ﺍﻟﻮﺳﻴﻂ)).
Ma’ana: ((Fadakarwa: Gazaalii ya ce: Na ji sashin
malaman hadithi na cewa: Wannan hadithi ya zo ne a
kan cewa yana sake hannayensa ne zuwa girjinsa, ba
wai yana sake su ba ne, sannan daga baya ya daga
su zuwa girji ba. Ibnus Salaah ya hikaito shi cikin
“Mushkilul Wasiit”)).
(2) Idan wani kuma ya ce: To ai an samu daga cikin
magabata wadanda suka yi salla hannayensu a sake,
don mene ne za a ce da mu yanzu: ba za mu yi salla
hannayenmu a sake ba?
To sai a ce da shi: Na farko dai ya kamata ka san
cewa ya kai dan’uwa! Annabi Muhammad mai tsira da
amincin Allah shi ne kadai wanda Allah Ya aiko shi
zuwa gare ka, bai aiko waninsa zuwa gare ka ba a
matsayin manzo, saboda haka ba daidai ba ne ka bar
umurninsa shi Annabi Muhammad ko kuma ka bar
aikinsa, sannan ka je kana riko da umurni ko da aikin
wani koma wane ne shi a wannan duniya!
Abu na biyu: A lokacin da Sahabi Abdullahi Dan
Abbas ya yi yunkurin tabbatar da sunnar tamattu’i
cikin Hajji, an samu wasu mutane da suka ce da shi:
Ai Abubakar da Umar sun hana Mut’ar Hajji, shi kuwa
sai ya amsa ya ce da su: ((Wani dutse ya yi kusan
sauko muku daga sama! Ina ce muku: Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah ya ce, sannan kuna ce da
ni: Abubakar da Umar sun ce!)).
Wannan magana ta Abdullahi Dan Abbas asalinta na
cikin Musnadu Ahmad hadithi na 3,121, da
Almuujamul Ausat na Tabaraanii hadithi na 21, da
Jami’u bayanil ilmi na Ibnu Abdil Bar hadithi na
2,377, da Alfaqih wal Mutafaqqih na Khatiibul
Bagdaadii hadithi na 380.
Abu na uku shi ne: Barin aiki da maganar Annabi ko
aikinsa zuwa yin aiki da maganar wani ko aikinsa
saba wa Ijma’in Al’ummah ne, shi kuwa yin hakan
haramun ne a bisa ittifakin dukkan malaman Duniya,
idan Annabi ya yi umurni da a yi Kablu a cikin salla
sannan ka ji wani kuma yana cewa a yi sadlu domin
ai sadlu ba ya bata salla to lalle wannan mutum ya yi
haramun ya zama mai sabon Allah a bisa ijma’in
Maluman Musulunci!
Ya zo cikin littafin Iiqazul Himam shafi na 68 cewa
Imamush Shafi’ii ya ce: ((Musulmi sun yi Ijma’i a kan
cewa duk wanda sunnar Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah ta bayyana gare shi, to, ba ya halatta
gare shi ya bar ta saboda yin riko da maganar wani)).
(3) Idan wani ya ce: To ai sake hannaye cikin salla
shi ne mazhabar Imam Malik, tunda mu kuwa
Malikiyyah ne ke nan dukkan abin da Imam Malik ya
yi na Addini shi ne mu ma za mu yi!!
To sai a ce da shi: Na farko dai ya kamata ka san
cewa Allah Madaukakin Sarki bai aiko maka Imam
Malik a matsayin manzo ba, a’a Ya aiko maka Annabi
Muhammad ne a matsayin manzo zuwa gare ka kai
da sauran mutanen Duniya baki daya, shi kuwa
Annabi Muhammad babu inda ya ce da kai ka yi salla
hannayenka a sake, a’a abin da ya ce da kai shi ne:
Ka dora damanka a kan hagunka cikin sallanka. Ta
kaka za ka bar nasa ka riki na wani komin girmansa
kuwa a idanunka?
A bu na biyu: cewa da ka yi: mazhabar Imam Malik
ita ce: yin salla hannaye a sake, magana ce mara
dikka, saboda shi Imam Malik yana da fatawowi
daidai har guda hudu ne cikin wannan mas’alar, ba
wai fatawa daya kawai ba.
Babban Malami cikin mazhabar malikiyyah Imamul
Baajii ya ce cikin littafinsa Almuntaqaa 1/281: Imam
Malik yana da fatawowi hudu da aka ruwaito daga
gare shi cikin wannan mas’alar: Fatawar farko:
Ash’hab ya ruwaito daga gare shi cewa: Babu laifi a
dora dama a kan hagu cikin sallar nafila da farilla.
Fatawa ta biyu: Mutarrif da Ibnul Maajishuun da kuma
almajiransa na Iraq sun ruwaito daga gare shi cewa:
Dora dama a kan hagu cikin salla mustahabbi ne.
Fatawa ta uku: Mutanen Iraq sun ruwaito daga
Malikawa daga shi Imam Malik cewa: Kada a dora
dama a kan hagu cikin salla. Fatawa ta hudu: Ibnul
Qaasim ya ruwaito daga gare shi cewa: makruuhi ne
a dora dama a kan hagu cikin sallar farilla, amma
babu laifi a yi hakan cikin sallar nafila.
A nan ai kun ga ya kamata a ce imma Malikiyyar za a
yi, to sai a yi wacce ta dace da sunnar Annabi mai
tsira da amincin Allah, ba wai wacce ta saba wa
sunnar Muhammadur Rasuulul Lahi ba, Allah ya
taimake kan yin aiki da sahihiyar Sunnar ManzonSa.
(4) Idan wani ya ce: To mene ne fahimtar
Malamanmu na Da’awah da Aqidah kuma cikin
wannan mas’alar?
Sai a ce da shi: Fahimtar mutanen da muka sani daga
cikinsu ita ce: Yin salla hannaye a sake abu ne da
yake sabanin Sunnah. Misali: Sheik Abdulaziz Bin
Baz ya ce cikin littafinsa na fatawa 11/144:-
(( ﺍﻟﺜﺎﺑﺖ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﻧﻪ ﻳﻘﺒﺾ ﻳﺪﻳﻪ
ﺣﺎﻝ ﻗﻴﺎﻣﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺓ …ﺍﻣﺎ ﺇﺭﺳﺎﻝ ﺍﻟﻴﺪﻳﻦ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺓ
ﻓﻤﻜﺮﻭﻩ ﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻓﻌﻠﻪ ﻟﻜﻮﻧﻪ ﺧﻼﻑ ﺍﻟﺴﻨﺔ )).
Ma’ana: ((Abin da ya tabbata daga Annabi mai tsira
da amincin Allah shi ne cewa: Yana kame
hannayensa ne lokacin da yake tsaye cikin
salla ..Amma sake hannaye a cikin salla makruhi ne,
yin sa bai kamata ba, saboda kasancewarsa sabanin
Sunnah)).
Sannan ya sake cewa cikin wannan littafin nasa
11/145:-
(( ﻭﺑﻤﺎ ﺫﻛﺮﻧﺎﻩ ﺗﻌﻠﻤﻮﻥ ﺍﻥ ﺇﺭﺳﺎﻝ ﺍﻟﻴﺪﻳﻦ ﻻ ﻳﻘﺪﺡ ﻓﻲ ﺍﺳﻼﻡ
ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ، ﻭﻻ ﻓﻲ ﺍﻛﻞ ﺫﺑﻴﺤﺘﻪ ﻟﻜﻨﻪ ﻣﻜﺮﻭﻩ ﻭﻣﺨﺎﻟﻒ ﻟﻠﺴﻨﺔ ﻻ
ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻓﻌﻠﻪ )).
Ma’ana: ((Saboda abin da muka ambata din nan ne za
ku san cewa: Sake hannaye ba ya soke Musuluncin
Musulmi, haka nan cin yankansa, sai dai kuma shi
makruhi ne, kuma abu ne da ya saba wa Sunnah, ba
ya kamata a yi shi)).
Sannan ya sake cewa cikin wannan littafi nasa
29/239:-
(( ﻫﺬﺍ ﻣﻜﺮﻭﻩ، ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﺿﻤﻬﻤﺎ ﻭﺟﻌﻠﻬﻤﺎ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﺪﺭ، ﻭﺟﻌﻞ
ﺍﻟﻴﻤﻨﻰ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻴﺴﺮﻯ ﻭﺍﻟﺮﺳﻎ ﻭﺍﻟﺴﺎﻋﺪ؛ ﻻﻧﻪ ﻗﺪ ﺛﺒﺖ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺚ ﺳﻬﻞ ﺑﻦ ﺳﻌﺪ، ﻭﻭﺍﺋﻞ ﺑﻦ
ﺣﺠﺮ، ﻭﻫﻠﺐ ﺍﻟﻄﺎﺋﻲ ﻣﺎ ﻳﺪﻝ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ . ﺍﻣﺎ ﺍﻹﺭﺳﺎﻝ ﻓﻼ ﺩﻟﻴﻞ
ﻋﻠﻴﻪ، ﺑﻞ ﻫﻮ ﺧﻼﻑ ﺍﻟﺴﻨﺔ )).
Ma’ana: ((Wannan makruhi ne, abin da yake Sunnah:
Taro su da sanya su a kan kirji, da kuma sanya dama
a kan tafin hagu da wuyan hannu, da dantse, saboda
ya tabbata daga Annabi mai tsira da amincin Allah
daga hadithin Sahl Dan Sa’ad, da Waa’il Dan Hujur, da
Hulb Attaa’ii abin da yake nuna hakan. Amma sake
hannaye babu wani dalil a kansa, kai a gaskiya ma
shi sabanin Sunnah ne)).
(5) Idan wani ya ce: Ko a cikin shugabannin
Mazhabar Imam Malik akwai wadanda ke ganin cewa
da zarar an samu wata fatawa a cikin Mazhabar
malikiyyah wacce ta saba wa sahihiyar sunnar
Manzon Allah, to, a yi watsi da ita, a koma a yi riko
da sahihiyar sunnar Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah kawai?
Amsa a nan ita ce: Lalle akwai su da yawa, a gaskiya
ma ni babu wani shahararre daga cikinsu da na sani
yake cewa: Bayan Bamalike ya fahimci cewa
sahihiyar Sunnah ta saba wa malikancinsa ya yi
watsi da sahihiyar Sunnar ya cigaba da yin aiki da
abin da ya zo cikin mazhabarsa kawai!! Ni ban san
wani mash’huri da ya fidi irin wannan magana mara
kan gado ba. Gaskiyan lamari shi ne: Abin da
shugabannin mazhaba suke cewa shi ne: Duk lokacin
da wani kaulin mazhaba ya yi karo da sahihiyar
Sunnah to sai a jingine mazhabar a yi aiki da
sahihiyar Sunnah. Imam Malik da kansa yana cewa
kamar yadda ya zo cikin littafin Tartiibul Madaarik
1/182:-
(( ﺍﻧﻤﺎ ﺍﻧﺎ ﺑﺸﺮ ﺃﺧﻄﺊ ﻭﺃﺻﻴﺐ، ﻓﺎﻧﻈﺮﻭﺍ ﻓﻲ ﺭﺃﻳﻲ ﻓﻜﻞ ﻣﺎ
ﻭﺍﻓﻖ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺨﺬﻭﻩ، ﻭﻛﻞ ﻣﺎ ﻟﻢ ﻳﻮﺍﻓﻖ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ
ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺎﺗﺮﻛﻮﻩ )).
Ma’ana: ((Ni ba kowa ba ne face mutum, ina yin kure
kuma ina yin daidai, sai ku rika yin nazari cikin
ijtihadina, dukkan abin da ya dace da Alkur’ani da
Sunnah sai ku rike shi, kuma dukkan abin da bai dace
da Alkur’ani da Sunnah ba sai ku bar shi)).
Sannan babban malami Jamaalud Dinil Qaasimii ya
ce cikin littafinsa: Attahdiithu Fi Fununi Mustalahil
Hadith shafi na 245, da babban malami Saalih Bin
Muhammad Alfullaanii cikin littafinsa: Iiqaazu Himami
Ulil Absar shafi na 89: dukkansu biyun sun ce:
Babban malami cikin mazhabar Malikiyyah
Muhammad Almaqqarii ya ce cikin littafinsa na
Qwa’idul Fiqhi:-
(( ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﻇﺎﻫﺮ ﻧﺺ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﻣﻊ ﻣﺨﺎﻟﻔﺘﻪ ﻷﺻﻮﻝ
ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ﻋﻨﺪ ﺣﺬﺍﻕ ﺍﻟﺸﻴﻮﺥ. ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﺎﺟﻲ: ﻻ ﺍﻋﻠﻢ ﻗﻮﻻ ﺍﺷﺪ
ﺧﻼﻓﺎ ﻋﻠﻰ ﻣﺎﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺍﻻﻧﺪﻟﺲ؛ ﻻﻥ ﻣﺎﻟﻜﺎ ﻻ ﻳﺠﻴﺰ ﺗﻘﻠﻴﺪ
ﺍﻟﺮﻭﺍﺓ ﻋﻨﻪ ﻋﻨﺪ ﻣﺨﺎﻟﻔﺘﻬﻢ ﺍﻷﺻﻮﻝ ﻭﻫﻢ ﻻ ﻳﻌﺘﻤﺪﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ .
ﺍﻧﺘﻬﻰ. ﻭﻗﺎﻝ ﺃﻳﻀﺎً : ﻗﺎﻋﺪﺓ: ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺭﺩ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻤﺬﻫﺐ
ﻋﻠﻰ ﻭﺟﻪ ﻳﻨﻘﺺ ﻣﻦ ﺑﻬﺠﺘﻬﺎ ﻭﻳﺬﻫﺐ ﺑﺎﻟﺜﻘﺔ ﺑﻈﺎﻫﺮﻫﺎ؛ ﻓﺎﻥ
ﺫﻟﻚ ﻓﺴﺎﺩ ﻟﻬﺎ ﻭﺣﻂ ﻣﻦ ﻣﻨﺰﻟﺘﻨﺎ، ﻻ ﺍﺻﻠﺢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻤﺬﻫﺐ
ﻟﻔﺴﺎﺩﻫﺎ، ﻭﻻ ﺭﻓﻌﻬﺎ ﺑﺨﻔﺾ ﺩﺭﺟﺎﺗﻬﺎ، ﻓﻜﻞ ﻛﻼﻡ ﻳﺆﺧﺬ ﻣﻨﻪ
ﻭﻳﺮﺩ ﺍﻻ ﻣﺎ ﺻﺢ ﻟﻨﺎ ﻋﻦ ﻣﺤﻤﺪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﺑﻞ ﻻ
ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻟﺮﺩ ﻣﻄﻠﻘﺎ؛ ﻻﻥ ﺍﻟﻮﺍﺟﺐ ﺍﻥ ﺗﺮﺩ ﺍﻟﻤﺬﺍﻫﺐ ﺍﻟﻴﻬﺎ )).
Ma’ana: ((Bai halatta bin zahirin nassin Imami tare da
sabawarsa ga jigogin Shari’ah (Qur’ani da Hadithi) a
wurin korarrun Shaihunai. (Imam) Baajii ya ce: Ban
san wani kauli da ya fi tsananin saba wa Malik ba
kamar (kaulin) mutanen Andulus ba, saboda Malik ba
ya halattar da bin masu ruwaya daga gare shi ba a
lokacin da suka saba wa Jigogi, su ba sa dogara a
kan haka. Intaha. Sannan (Imam Baajii) ya sake
cewa: Qaa’idah: Bai halatta a yi raddin Hadithai zuwa
ga mazhaba ta fiskar da zai rage wani abu na
armashinsu, kuma ya tafiyar da amincewa da
zahirinsu, domin hakan bata su ne da kuma
wulakanta matsayinsu. Kada Allah Ya kyautata
mazhabobi ta hanyar bacinsu (watau su hadithan)
kada (Allah Ya daukaka mazhabobin) ta hanyar karya
darajarsu (su hadithan). Dukkan wata magana Ana
iya aiki da ita, ana kuma iya yin watsi da ita, amma
banda abin da ya inganta a wurinmu daga
Muhammad mai tsira da amincin Allah, ko kadan bai
halatta a yi raddin (maganarsa), domin abin da ke
wajibi shi ne: Yin raddin mazhabobi zuwa gare ta))
(watau maganar Annabi mai tsira da amincin Allah).
(6) Idan wani ya ce: Dalilan nan duka da ka kawo na
cewa: dora dama a kan hagu cikin salla shi ne
Sunnah, sake hannaye kuwa sabanin Sunnah ne,
wasu mutane za su ce ba su gamsu da su ba, hasali
ma za su ce dukkan hadithan masu rauni ne, saboda
haka yin salla hannaye a sake shi ne daidai domin
shi ne abin da suka sani a mazhabar Malikiyya!!!
To, sai a ce da shi: Na farko dai da ma ba dukkan
gaskiyar da masu wa’azi ke fada ba ne mutane ke
karba, Annabawa da Manzanni sun gaya wa
jama’arsu gaskiya, amma an samu mutane da yawa
wadanda suka karyata su, suka yi watsi da gaskiyar
da suka fada musu. Wannan shi ya sa za ka ga ‘yan
bidi’ah da yawa suna karyata ingantattun hadithan
Buhari da Muslim suka ruwaito cikin sahihansu,
matukar dai hadithan sun saba wa abin da Dagutansu
suka dora su a kan shi iyazan billah!
A bu na biyu shi ne: Ciwon son zuciya na da wahalar
waraka, wannan shi ya sa duk yadda masu wa’azi
suka yi kokarin fahimtar da Kiristoci cewa aqidarsu ta
cewa Allah yana da Da watau Isa, kuma shi Allah
Dayan uku ne! watau: shi ne Allah Uba, sannan kuma
akwai Allah Da! Sannan kuma akwai Allah Ruhu Mai
tsarki! Duk lokacin da masu wa’azi suka yi kokarin
fahimtar da su cewa wannan kure ne bayyananne sai
ka ga cewa suna ta kawo tawilce-tawilce da wasu
shubuhohi domin tabbatar da ra’ayinsu marar
makama da hujja!!
Haka nan in ka dubi yan bidi’ah nau’i daban-daban
da ake da su cikin Al’ummar Musulmi za ka rika
ganin yadda suke zaburowa da karfi suna kare son
zuciyarsu. Misali yanzu in ka yi kokarin fahimtar da
batijjane cewa: aqidarsa ta cewa Salatul Fatihi
saudaya tana daidai da Alkur’ani sau dari shida
wanda wannan yana nufin ke nan Salatul Fatihi ta fi
Alkur’ani sau dari biyar da casa’in da tara!! In ka
shaida musu cewa wannan akidah tasu wani nau’i ne
na ilhadi da raina Littafin Allah Madaukakin Sarki, to
nan da nan za ka ga cewa sun yi ca a kanka da
zage-zage, da bace-bace, kuma za ka ga cewa sun
nace suna ta yin tawilce-tawilce domin su tabbatar
da son zuciyarsa!!
To amma irin wannan hayaniya ta yan bidi’ah, da ‘yan
bin son zuciya sam bai kamata ba a ce za ta hana
masu wa’azi ci gaba da shiryar da Al’ummah zuwa ga
sahihiyar sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah
ba.
Muna rokon Allah muna kaskantar da kai a gabanSa
da ya tausaya Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya
ba mu ikon bin ta, Ya kuma nuna mana karya karya
ce Ya ba mu ikon guje mata.
Ameeeeen.
@Danjagale’s Blog.
http://t.co/2wFeKmjyQW

HUKUNCIN KARBAR KYAUTAR IDIN KIRISMETI DA CIN ABINCIN WANNAN RANA KAMAR YADDA SALAFUS SAA’LIH SUKA YI BAYANI.

1- Da yake Alhamis mai zuwa ne Kiristoci za su fara
abin da suke kira bukin kirsimeti (idin kirsimeti)
wanda suke yin shi ko dai a ranar 25/12 M ko kuwa
a ranar 7/1 M.
2- Sannan da yake a Nigeria ana zaman cakuda ne
tsakanin su Kiristoci da kuma al’ummar Musulmi.
3- Sannan da yake shi Musulunci addini ne da ya
bayyanar da hukuncin dukkan wani lamari da ya shafi
rayuwar dan Adam, ko dai ta hanyar nassi, ko ta
hanyar zahiri, ko ta hanyar ishaarah da iimaai.
4- Sannan da yake akwai masu bidi’ah da dama da ke
halatta abin da Shari’ah ba ta halatta ba, ko haramta
abin da Shari’ah ba ta haramta ba, lalle ya dace a yi
wa al’ummar Musulmi bayanin hukuncin abin da ya
shafi wannan Idi na Kirsimeti ta bangarorinsa da ke
iya shafar wasu al’ummar Musulmi.
**************************
To amma kafin mu shiga bayanin wadannan
hukunce-hukunce ya kamata Musulmi su san
abubuwa kamar haka:-
Na farko: Shi dai bukin kirsimeti wata bidi’ah ce da
bata da kiristoci suka kirkira sannan suka maida ita
wata ibada da ake samun lada ta hanyar yin ta –
kamar dai yadda wasu Musulmi suka kirkiri bidi’ar
idin mauludi- Kiristoci sun kirkiri wannan bidi’ar ce
kuwa a shekarar miladiyyah ta 360, watau a cikin
karni na hudu bayan haifuwar Annabi Isa alaihis
salam.
Na biyu: Ya kamata kowa ya san cewa ba ya halatta
Musulmi ya yi tarayya da wadanda ba musulmi ba
cikin bukukuwansu na idi, watau ta hanyar halartan
wasu tarurruka da za su kira, ko ta hanyar ba su wani
taimako domin karfafa idodin nasu, wannan dai shi
ne hanyar Salafus Salih -Sahabbai, da Taabi’ai, da
Taabi’uttaabi’in- dalili kuwa shi ne:-
Imamul Baihaqii ya ruwaito cikin As-Sunanul Kubraa
hadithi na 19,334 cewa Sayyidina Umar Dan Khattab
Allah Ya kara masa yarda ya ce:-
(( ﺍﺟﺘﻨﺒﻮﺍ ﺃﻋﺪﺍﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﻋﻴﺪﻫﻢ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Ku nisanci makiya Allah cikin idinsu)).
Intaha.
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Tamiyyah ya ce -kamar
yadda ya zo cikin Al-Mustadrak Alaa Fataawaa Ibnu
Tamiyyah 1/108, da Mukhtasarul Fataawaa
Misriyyah1/517 :-
(( ﻭﻟﻴﺲ ﻟﻠﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺍﻥ ﻳﻌﻴﻨﻮﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺃﻋﻴﺎﺩﻫﻢ ﻻ ﺑﺒﻴﻊ ﻣﺎ
ﻳﺴﺘﻌﻴﻨﻮﻥ ﺑﻪ ﻋﻠﻰ ﻋﻴﺪﻫﻢ ﻭﻻ ﺑﺎﺟﺎﺭﺓ ﺩﻭﺍﺑﻬﻢ ﻟﻴﺮﻛﺒﻮﻫﺎ ﻓﻲ
ﻋﻴﺪﻫﻢ ﻻﻥ ﺃﻋﻴﺎﺩﻫﻢ ﻣﻤﺎ ﺣﺮﻣﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻟﻤﺎ ﻓﻴﻬﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻔﺮ ﻭﺍﻟﻔﺴﻮﻕ ﻭﺍﻟﻌﺼﻴﺎﻥ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Musulmi ba su da damar su taimaka musu
cikin idodinsu, ko dai ta hanyar sayar musu da abin
da za su karfafu da shi, ko ta hanyar ba da hayar
dabbobinsu domin su hau su cikin idinsu, saboda
idodinsu na daga cikin abin da Allah Madaukakin
Sarki da kuma manzonSa mai tsira da amincin Allah
suka haramta, saboda abin da yake cikinsu na kafirci
da fasikanci da kuma sabo)). Intaha.
Na uku: Babu wani wanda ya isa ya bugi kirji a
duniyan nan ya ce: ga tabbatacciyar wata da rana da
aka haifi Annabi Isa alaihis salam a cikinta, sai dai
kowa ya fadi abin da yake zato kawai, wannan shi ya
sa ma Kiristoci masu yin bukin ranar Kirsimeti watau
ranar haifuwar Annabi Isa alaihis salam suka yi
sabani dangane da ranar da za a yi wannan bukin
zuwa mazhabobi biyu:-
Mazhabar farko: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 25
ga watan December, wannan ita ce mazhabar da
Catholic, da Protestant, da kuma mafi yawan
bangarorin Kiristoci ke bi.
Mazhaba ta biyu: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 7
ga watan January, wannan ita ce mazhabar da
bangarorin Orthodox ke bi.
Na hudu: Kiristoci kafurai ne kamar yadda Yahudawa
da Majusawa da sauran masu bautar gumaka suke
kafurai, babu sabani cikin wannan mas’ala cikin
shari’ar Musulunci.
Na biyar: Ya kamata a san cewa akwai wasu kafuran
da Musulunci ya kebanta su da wasu hukunce-
hukunce saboda tabbatar wa Musulmi wata maslaha,
wadannan kuwa su ne: Yahudawa, da Kiristoci, su
wannan nau’i na kafurai Musulunci ya halatta wa
Musulmi cin yankansu, da kuma auren matansu,
sabanin mabiya addinin majusu, ko mabiya addinin
Hindu, ko mabiya addinin Budha, ko mabiya sauran
addinai na bautan gumaka.
*************************
Idan Musulmi sun fahimci wannan sai mu shiga
bayanin mas’alarmu da muke son yi wa jama’a
bayaninta, muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya
taimake mu.
HUKUNCIN KARBAN KYAUTUTTUKAN KAFURAI A RANAR IDINSU:
Su kyaututtukan da kafurai -Ahlul kitabi ko wasun
Ahlul kitabi- ke ba wa Musulmi a ranakun idinsu na
kafurci da bidi’ah sun kasu kashi biyu ne:-
Na farko: Kyaututtukan da suke ba nama ba ne da
ake bukatar yankawa, watau kamar irinsu: halawa, da
tufafi, da kayan marmari da sauransu.
Na biyu: Kyaututtukan da suke nama ne da ke
bukatar a yi masa yanka irin ta Shari’ah.
To shi na farkon, watau kyaututtukan da suke ba
nama ba ne da ke bukatar yanka irin ta Shari’ah, babu
sabani tsakanin Salafus Salih -a dai iya saninmu-
cikin halaccin karbarsu, saboda dalilai kamar haka:-
1- Imamul Baihaqii ya ruwaito athari na 18,644 daga
Muhammad Dan Siiriin cewa:-
(( ﺃﺗﻲ ﻋﻠﻲ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻬﺪﻳﺔ ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ، ﻓﻘﺎﻝ: ﻣﺎ ﻫﺬﻩ؟ ﻗﺎﻟﻮﺍ : ﻳﺎ
ﺍﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻫﺬﺍ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ . ﻗﺎﻝ : ﻓﺎﺻﻨﻌﻮﺍ ﻛﻞ ﻳﻮﻡ
ﻓﻴﺮﻭﺯ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((An zo wa Sayyidina Aliyyu Dan Abii Taa’lib
Allah Ya kara masa yarda da kyautar (idin) Nairuuz,
sai ya ce: mene ne wannan? Sai suka ce: Ya Amirar
Muu’miniin! Wannan ranar Nairuuz ce. Sai ya ce: (in
haka abin yake) ku rika yin Fairuuz a ko wace rana)).
Intaha.
2- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito cikin
Musannaf athari na 24,371, da Imam Ishaq Ibnu
Raa’huyyah cikin Musnad athari na 1,606 daga
Qaa’bus Dan Zibyaan daga shi mahaifin nasa cewa
wata mace ta tambayi Nana A’isha Allah Ya kara mata
yarda ta ce:-
(( ﺍﻥ ﻟﻨﺎ ﺍﻛﺎﺭﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺠﻮﺱ ﻭﺍﻧﻪ ﻳﻜﻮﻥ ﻟﻬﻢ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻓﻴﻬﺪﻭﻥ ﻟﻨﺎ،
ﻓﻘﺎﻟﺖ: ﺍﻣﺎ ﻣﺎ ﺫﺑﺢ ﻟﺬﻟﻚ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻓﻼ ﺗﺄﻛﻠﻮﺍ ﻭﻟﻜﻦ ﻛﻠﻮﺍ ﻣﻦ
ﺃﺷﺠﺎﺭﻫﻢ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ
Ma’ana: ((Muna da ‘yan kodago daga cikin Majusawa,
sannan kuma suna da ranar idin da suke aika mana
da kyaututtuka. Sai ta ce: Amma abin da aka yanka
saboda wannan ranar to kada ku ci, to amma ku ci
daga ‘ya’yan itatuwansu)). Intaha.
3- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito a cikin
Musannaf athari na 24,372 daga Abuu Barzah cewa:-
(( ﻛﺎﻥ ﻟﻪ ﺳﻜﺎﻥ ﻣﺠﻮﺱ ﻓﻜﺎﻧﻮﺍ ﻳﻬﺪﻭﻥ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﻴﺮﻭﺯ
ﻭﺍﻟﻤﻬﺮﺟﺎﻥ ﻓﻜﺎﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﻷﻫﻠﻪ : ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﻓﺎﻛﻬﺔ ﻓﻜﻠﻮﺍ ﻭﻣﺎ
ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﻓﺮﺩﻭﻩ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Yana da wasu mazauna Majusawa, kuma
sun kasance suna aika masa da kyautuka a lokacin
Nairuuz da Mihrajan, sannan ya kasance yana gaya
wa iyalansa cewa: Kyautar da ta kasance ta kayan
marmari ne to ku ci, wacce kuma ta kasance ba
hakan ba, to ku mayar da ita)). Intaha.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi taliki a kan
wadannan hujjojin a cikin littafinsa mai suna
Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqiim 2/554-555 ya ce:-
(( ﻓﻬﺬﺍ ﻳﺪﻝ ﻋﻠﻰ ﺍﻧﻪ ﻻ ﺗﺄﺛﻴﺮ ﻟﻠﻌﻴﺪ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﻨﻊ ﻣﻦ ﻗﺒﻮﻝ
ﻫﺪﻳﺘﻬﻢ، ﺑﻞ ﺣﻜﻤﻬﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻴﺪ ﻭﻏﻴﺮﻩ ﺳﻮﺍﺀ؛ ﻻﻧﻪ ﻟﻴﺲ ﻓﻲ
ﺫﻟﻚ ﺇﻋﺎﻧﺔ ﻟﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﺷﻌﺎﺋﺮ ﻛﻔﺮﻫﻢ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Wannan duka yana nuni ne a kan cewa: Idi
ba yi da wani tasiri a kan hana karban kyautarsu, a’a
hukuncin karban kyautarsu ba yi da wani bambanci
tsakanin lokacin Idi da kuma lokacin da ba na Idi ba,
saboda babu wani abu na taimakon addininsu a cikin
karban kyautarsu)). Intaha.

TA’ALIKI:
Da wannan ne za mu fahimci cewa: Maluman
Musulunci sun hana cin yankan da Majusawa suka yi
domin bukukuwan idinsu, to amma fa ba wai sun
hana cin yankan ba ne saboda kasancewarsa yankan
da aka yi domin bukin idin kafurai ba, a’a an hana cin
yankan ne saboda kasancewarsa yankan Majusawan
da ba sa cikin mutanen nan ne da ake kira Yahudawa
ko ake kira Kiristoci, dukkan kuma kafurin da ba ya
cikin abin da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci
to ba a cin yankansa.
HUKUNCIN CIN NAMAN DABBAR DA YAHUDAWA KO
KIRISTOCI SUKA YANKA DA HANNAYENSU SABODA
YIN BUKUKUWAN IDINSU:
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi bayani game da
cin abin da Yahudawa ko Kiristoci suka yanka saboda
bukukuwan idinsu, a cikin littafinsa mai suna
Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqim 2/555,558 ya ce:-
(( ﻭﺍﻧﻤﺎ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻥ ﻳﺆﻛﻞ ﻣﻦ ﻃﻌﺎﻡ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻓﻲ ﻋﻴﺪﻫﻢ
ﺑﺎﺑﺘﻴﺎﻉ ﺍﻭ ﻫﺪﻳﺔ ﺍﻭ ﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﻣﻤﺎ ﻟﻢ ﻳﺬﺑﺤﻮﻩ ﻟﻠﻌﻴﺪ . ﻓﺄﻣﺎ ﺫﺑﺢ
ﺍﻟﻤﺠﻮﺱ ﻓﺎﻟﺤﻜﻢ ﻓﻴﻬﺎ ﻣﻌﻠﻮﻡ ﻓﺈﻧﻬﺎ ﺣﺮﺍﻡ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻌﺎﻣﺔ . ﻭﺃﻣﺎ ﻣﺎ
ﺫﺑﺤﻪ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻻﻋﻴﺎﺩﻫﻢ ﻭﻣﺎ ﻳﺘﻘﺮﺑﻮﻥ ﺑﺬﺑﺤﻪ ﺍﻟﻰ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ
ﻧﻈﻴﺮ ﻣﺎ ﻳﺬﺑﺢ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻣﻦ ﻫﺪﺍﻳﺎﻫﻢ ﻭﺿﺤﺎﻳﺎﻫﻢ ﻣﺘﻘﺮﺑﻴﻦ
ﺑﻬﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ، ﻭﺫﻟﻚ ﻣﺜﻞ ﻣﺎ ﻳﺬﺑﺤﻮﻥ ﻟﻠﻤﺴﻴﺢ ﻭﺍﻟﺰﻫﺮﺓ،
ﻓﻌﻦ ﺍﺣﻤﺪ ﺭﻭﺍﻳﺘﺎﻥ : ﺍﺷﻬﺮﻫﻤﺎ ﻓﻲ ﻧﺼﻮﺻﻪ : ﺍﻧﻪ ﻻ ﻳﺒﺎﺡ ﺍﻛﻠﻪ
ﻭﺍﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﻢ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ . ﻭﻧﻘﻞ ﺍﻟﻨﻬﻲ ﻋﻦ ﺫﻟﻚ ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ
ﻭﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: (Cin abincin Ahlul Kitabi a lokacin idinsu ga
abin da dama ba su yanka shi saboda Idi ba, yana
halatta ne ta hanyar saye da kudi, ko kuwa kyauta, ko
wanin haka. Amma abin da Majusawa suka yanka
hukuncinsa sananne ne, watau haramun ne a wurin
dukkan malamai, to amma abin da Ahlul Kitabi suka
yanka saboda idinsu, da kuma abin da suke yin ibada
ta hanyar yanka shi ga wanin Allah’ kamar abin da
suke yankawa saboda Almasihu, da Zahrah, irin dai
abin da Musulmi suke yankawa na Hadaya, da Layya,
domin neman kusantar Allah da shi, to, Imam Ahmad
yana da fatawowi biyu game da hakan, fatawar farko
wacce ita ce ta fi shahara: Wannan ba ya halatta a ci
shi koda kuwa ba a ambaci sunan wanin Allah a
kansa ba. An nakalto hana cin wannan yankan ma
daga Nana A’isha, da Abdullahi Dan Umar.. Fatawa ta
biyu ita ce: Cin wannan yankan makruuhi ne ba
haramun ba. Wannan ita ce mazhabar Malikiyyah,
Imam Malik ya kyamaci cin abin da Ahlul Kitabi suka
yanka saboda Coci-Cocinsu, ko saboda idinsu amma
ba tare da ya haramta hakan ba)). Intaha.
Sannan har yanzu Sahikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya
ce a cikin Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqim 2/559 :-
(( ﻭﻧﻘﻠﺖ ﺍﻟﺮﺧﺼﺔ ﻓﻲ ﺫﺑﺎﺋﺢ ﺍﻷﻋﻴﺎﺩ ﻭﻧﺤﻮﻫﺎ ﻋﻦ ﻃﺎﺋﻔﺔ ﻣﻦ
ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻢ، ﻭﻫﺬﺍ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺫﺍ ﻟﻢ ﻳﺴﻤﻮﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ،
ﻓﺎﻥ ﺳﻤﻮﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﻋﻴﺪﻫﻢ ﺍﻭ ﻏﻴﺮ ﻋﻴﺪﻫﻢ ﺣﺮﻡ ﻓﻲ ﺍﺷﻬﺮ
ﺍﻟﺮﻭﺍﻳﺘﻴﻦ، ﻭﻫﻮ ﻣﺬﻫﺐ ﺍﻟﺠﻤﻬﻮﺭ، ﻭﻫﻮ ﻣﺬﻫﺐ ﺍﻟﻔﻘﻬﺎﺀ ﺍﻟﺜﻼﺛﺔ
ﻓﻴﻤﺎ ﻧﻘﻠﻪ ﻏﻴﺮ ﻭﺍﺣﺪ، ﻭﻫﻮ ﻗﻮﻝ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ
ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ، ﻭﻫﻮ ﻗﻮﻝ ﺍﻛﺜﺮ ﻓﻘﻬﺎﺀ ﺍﻟﺸﺎﻡ ﻭﻏﻴﺮﻫﻢ . ﻭﺍﻟﺜﺎﻧﻴﺔ : ﻻ
ﻳﺤﺮﻡ ﻭﺍﻥ ﺳﻤﻮﺍ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ، ﻭﻫﺬﺍ ﻗﻮﻝ ﻋﻄﺎﺀ ﻭﻣﺠﺎﻫﺪ
ﻭﻣﻜﺤﻮﻝ ﻭﺍﻻﻭﺯﺍﻋﻲ ﻭﺍﻟﻠﻴﺚ .(( ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((An ciro yin sauki a kan cin yanke-yanken
idodin (Yahudawa da Kiristoci) da makamantansu (su
yanke-yanken) daga wani sashi na Sahabbai Allah Ya
kara musu yarda amma fa wannan sai idan ba su
ambaci wanin Allah a lokacin yankan ba, in kuma har
sun ambaci wanin Allah a lokacin yankan to cin sa
ya haramta a cikin fatawa mafi shahara daga cikin
fatawowi biyu da Imam Ahmada yake da su a cikin
mas’alar, wannan kuwa shi ne mazhabar jumhur,
kuma shi ne mazhabar Fuqaha’un nan guda uku,
kamar yadda mutane da yawa suka ruwaito, kuma shi
ne maganar Aliyyu Dan zabii Taa’lib da waninsa a
cikin Sahabbai, daga cikinsu ma akwai Abud Dardaa,
da Abu Umamah, da Irbadh Dan Saa’riyah, da
Ubaa’dah Dan Saa’mit, kuma shi ne maganar
maluman Sham da wasunsu. Fatawar Imam Ahmad ta
biyu ita ce: Cin wannan yankan ba haramun ba ne
koda kuwa sun ambaci sunan wanin Allah a lokacin
yankan, wannan kuwa shi ne maganar Ataa’u, da
Mujaa’hid, da Makhuul, da Auzaa’ii, da kuma Laith)).
Intaha.
Taliki na farko:-
Za mu fahimta daga maganganun malaman da suka
gabata cewa: Abin da Yahudawa da Kiristoci suke
yankawa saboda bukukuwan idinsu yana kasuwa ne
zuwa kashi biyu:-
Na farko: Abin da suka ambaci sunan Allah yayin
yanka shi.
Na biyu: Abin da suka ambaci sunan wanin Allah
yayin yanka shi.
To ita tabbar da aka ambaci sunan Allah lokacin
yanka ta, Malamai sun kasu kashi biyu game da
hukuncin cinta.
Mazhabar farko: Sahabbai da yawa sun ba da damar
cin wannan nama. Maluman Malikiyyah, da Imam
Ahmad cikin ruwayah sun halattar da cinsa amma
tare da nuna kyama.
Mazhaba ta biyu: Nana A’isha, da Abdullahi Dan
Umar, da kuma Maluman Hanaa’bilah sun ce cin
wannan nama haramun ne.
Sannan ita kuma dabbar da aka ambaci sunan wanin
Allah lokacin yanka ta, watau kamar wacce aka
ambaci sunan Yesu Almasihu lokacin yanka ta,
wannan ma Malamai sun kasu kashi biyu game da
hukuncin cin wannan dabbar:-
Mazhabar farko: Cin wannan dabba bai halatta ba,
wannan shi ne abin da Aliyyu Dan Abii Taa’lib, da
Abud Dardaa’u, da Abuu Umamah, da Irbadh Da
Saa’riyah, da Ubaa’dah Dan Saa’mit, da Hanafiyyah,
da Malikiyyah, da Shafi’iyyah, da Hanaa’bilah, da mafi
yawan maluman kasar Sham, suk fada.
mazhaba ta biyu: Cin wannan dabba halal ne, wannan
shi ne abin da Ataa’u, da Mhjaa’hid, da Makhul, da
Auzaa’ii, da Laithu Dan Sa’ad, da kuma Imam Ahmad
cikin ruwaya suka fada.
Taliki na biyu:-
Za mu iya fahimta daga maganganun da suka gabata
cewa: Naman kasuwa da Musulmi ke yankawa da
hannayensu idan Kiristoci suka saya suka dafa a
matsayin abincin Kirsimeti, to wannan abincin halal
yake ga dukkan wanda suka ba da shi gare shi.
Wallahu A’alam.
****************************
HUKUNCIN CIN YANKAN KIRISTOCI DA YAHUDAWA A MAZHABAR MALIKIYYAH:
A karshen wannan makala tamu za mu yi bayanin
mene ne mash’hurin mazhabar Malikiyyah game cin
yankan Kiristoci da Yahudawa, saboda Musulmin
wannan kasa tamu Nigeria su kara fahimtar irin
banbancin da yake tsakanin abin da ke rubuce cikin
littattafan Mazhabar Malkiyyah, da kuma abin da
wasu jahilan ‘yan bidi’ah da suke ikirarin cewa su
masu bin Mazhabar Malikiyyah ne, alhali kuwa
hayaniyarsu kawai suke yi, son zuciyarsu ne kawai
suke bi, duk abin da jahilan shaihunansu suka ce to
shi ne addini a wurinsu. Allah ya tsare mu da sharrin
Shaidan.
Babban malamin Malikyyah Imamul Qurtubii ya ce
cikin littafinsa Aljaami’u Li Ahkaamil Qur’an 6/53:-
(( ﻭﻗﺎﻝ ﺟﻤﻬﻮﺭ ﺍﻻﻣﺔ ﺍﻥ ﺫﺑﻴﺤﺔ ﻛﻞ ﻧﺼﺮﺍﻧﻲ ﺣﻼﻝ ﺳﻮﺍﺀ ﻣﻦ
ﺑﻨﻲ ﺗﻐﻠﺐ ﺍﻭ ﻏﻴﺮﻫﻢ، ﻭﻛﺬﻟﻚ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ )).
Ma’ana: ((Jumhuurin Al’ummah sun ce: Lalle yankan
ko wane kirista halal ne, babu banbanci daga kabilar
Taglib ne ko daga wasunsu, haka nan su ma
Yahudawa)). Intaha.
Khalil Dan Ishaq ya ce cikin Mukhtasar Khalil shafi
na 90
(( ﻭﺍﻥ ﺳﺎﻣﺮﻳﺎ ﺍﻭ ﻣﺠﻮﺳﻴﺎ ﺗﻨﺼﺮ ﻭﺫﺑﺢ ﻟﻨﻔﺴﻪ ﻣﺴﺘﺤﻠﻪ، ﻭﺍﻥ
ﺍﻛﻞ ﺍﻟﻤﻴﺘﺔ ﺍﻥ ﻟﻢ ﻳﻐﺐ ))
Ma’an: ((koda ya kasance wani basaamire ne, ko
bamajuse ne da yazama kirista ya yanka abin da yake
halal a gare shi saboda kuma kan shi, koda kuwa
yana halatta cin mushe ne, matukar dai musulmi na
sane da cewa shi din ne ya yi yankan)).
Sannan ya zo cikin littafin Adhalulu Madaarik 2/92:-
(( ﻳﺠﻮﺯ ﻟﻠﻤﺴﻠﻢ ﻧﻜﺎﺡ ﺣﺮﺍﺋﺮ ﺍﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ .. ﻭﻛﺎﻥ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ
ﺑﺘﺰﻭﺟﻮﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﻭﺍﻟﻨﺼﺎﺭﻯ ﻛﺜﻴﺮﺍ ﺯﻣﻦ ﺍﻟﻔﺘﺢ .. ﻭﻧﻜﺢ
ﻋﺜﻤﺎﻥ ﻧﺼﺮﺍﻧﻴﺔ، ﻭﻧﻜﺢ ﻃﻠﺤﺔ ﻳﻬﻮﺩﻳﺔ )).
Ma’ana: ((yana halatta ga musulmi auren ‘yantattun
matan Ahlul Kitaabi.. Sahabbai sun kasance da yawa
suna auren matan Yahudawa da Kiristoci a lokacin da
ake cin kasashe da yaki.. Sayyidina Uthman ya auri
wata kirista, Sayyidina Talhah ya auri wata
bayahudiya)).
***********************
Muna rokon Allah Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce
ya ba mu ikon bin ta Ya kuma nuna mana karya
karya ce ya ba mu ikon guje mata.
Ameeeeen.
Via: http://t.co/2wFeKmjyQW