Wani likita ya kamu da Ebola a Najeriya

Aside

Hukumomi a Najeriya sun ce likitan da ya duba dan kasar Liberiyan nan mai dauke da cutar Ebola a jihar Lagos ya kamu da cutar.
Hakan na nufin shi ne mutum na biyu da aka tabbatar ya kamu cutar a Legas, wanda shi ne birni mafi yawan mutane a yammacin Afrika.
Ministan lafiya Onyebuchi Chukwu, wanda ya tabbatar da likitan na dauke da cutar, ya ce ana can ana yi masa magani, kuma a yanzu mutane 70 da aka yi amannar cewa sun yi mu’amala da dan kasar Liberiyar, ana kula da su inda takwas daga cikinsu aka kebe su.
An kuma dauki jinin karin wasu uku da alamu suka nuna suna dauke da cutar, domin yin gwaji.

An kirkiro wani Tabarau mai aiki da Kwamfuta domin taimakawa masu gani kadan-kadan.

Aside

Masu bincike a jami’ar Oxford da ke Ingila sun ce sun cimma wata gagarumar nasara wajen kirkiro wani tabarau mai aiki da kwamfuta domin taimkawa masu gani kadan-kadan.
Tabaran ya kan sa mutum ya ga mutanen da ke kusa da kuma wurin da mutum ya ke sosai.
Cibiyar makafi ta Birtaniya ta ce tabaran zai zama “Mai matukar amfani ga masu larurar idanu.”
A karon farko tabaran ya sa wasu masu matsalar gani sun ga karen da ke musu jagora.
Lyn Oliver mai shekaru 70 na da matsalar ido da ke kara tabarbarewa, kuma hakan yasa bata gani sosai.
Tana iya ganin gilmawar mutum ko wasu abubuwa, amma karenta mai suna Jess ne ke yi mata jagora.
Lyn na daya daga cikin ‘yan Burtaniya kusan miliyan biyu da ke fama da matsalar idanu, wanda hakan ke shafar yadda suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
Sai dai masu bincike na jami’ar Oxford sun kirkiro wani tabarau da zai inganta ganin irin wadannan mutane.
An sanya wa gilashin wata kamara ta musamman ta 3D kuma wata kwamfuta na tattara abubuwan da ta gani nan da nan ta tura ga gilashin tabaran, hakan na sa mutane da abubuwan da ke wuri su fito karara.
Lyn ta gwada tabaran wanda ake inganta shi, kuma gwajin baya-bayan nan na da muhimmanci sosai, domin ta ga abubuwa karara sosai fiye da a gwajin baya.
Dr. Stephen Hicks na jami’ar Oxford kuma wanda ke jagorantar aiki a kan tabaran ya ce, yanzu tabaran ya wuce matsayin bincike za a fara amfani da shi a gida.

An gano Rashin Tsaro a Kayan Gida Masu amfani da Yanar Gizo (Internet).

Aside

Kamfanin HP ya gano cewa za a iya kutse a cikin da yawa daga cikin kayayyakin da ke amfani da intanet a gidajen jama’a.
A kan wannan matsalar HP ke ganin ko ya dace a ce irin wadannan kayayyaki na gida sun kunshi muhimman bayanai na sirri na mutum ?
Sashen kula da tsaro na kamfanin na HP ya gudanar da bincike a kan wasu kayayyaki goma da ake amfani da su da intanet.
Wani kwararre kan sha’anin tsaro mai zaman kansa ya ce abin da aka gano abu ne mai tayar da hankali.
Kamfanin na HP bai bayyana sunayen kamfanonin da kayan nasu ke da wannan matsala ba, amma ya nuna kayayyaki goma da ya gudanar da binciken a kansu.
Talabijin mai komai-da-ruwanka da kyamarar jikin kwamfuta da fanfon ban ruwa a lambu da mukullin kofa, da na’urar kuwwa a gida da mabudin garejin mota da sauransu.
Damuwar daya daga cikin wadanda suka yi binciken, ita ce takwas daga cikin kayayyakin da aka yi gwajin a kansu ba sa bukatar mutum ya sa musu lambobin budewa masu sarkakiya ko wahalar ganowa.
Ya ce da dama daga cikinsu ana amfani da lambobi kamar 1234 ko 123456 ne kawai a bude su, kuma a gano bayanan mai amfani da su.
Masana na ganin cewa shin wajibi ne wadannan kayayyaki su tattara bayanan masu amfani da su, kafin su yi aiki ?
A farkon wannan watan, wani kamfanin harkokin tsaro ya bayyana cewa, kwan lantarkin da ke amfani da wi-fi da wani kamfanin Australia, Lifx ya yi, yana bayyana sunan mai amfani da shi da kuma mabudinsa, idan mai kutse ya yi amfani da wata na’ura da ta yi sojan gona kamar wani kwan lantarkin.
A shekarar da ta wuce, sai da kamfanin LG yayi gyara a kan talabijin din kamfanin mai komai-da-ruwanka, bayan da wani mutum ya gano cewa tana nazarin yanayin lokacin da yake kallo, kuma ta yada a intanet karara.

Kadangaren Dinosaurs mai gashi na yaduwa. wannan Dinosaurs yana da gashi a jikinsa, da dogayen kafafu, masu dauke da farata zako-zako

Aside

Wani binciken kimiyya ya gano cewa dukkan jikin kadangarun Dinosaurs na da gashi a jikinsu, ko kuma gashin zai iya fitowa a jikinsu.
An gano hakan ne a jikin kashin wani kadangaren Dinosaurs mai shekaru miliyan 150 a Siberia, wanda ya bayyana cewa ana iya samun kadangaren mai gashi a jikinsa fiye da yadda aka yi tsammani a baya.
Jagoran binciken ya shaidawa BBC cewa, sabon binciken da suka gudanar ya sauya baki dayan tunaninsu akan kadangaren na Dinosaurs.
An dai wallafa wannan bincike ne a jaridar mujallar Science.
Kadangaren Dinosaurs da aka yi binciken akan sa mai suna Kulindadromeus Zabaikalius ya na da tsahon mita 1, da dan gajeren hanci, da kuma dogayen kafafu, da gajerun kafada ka na kuma da farata guda biyar masu karfin gaske.
Hakoran sa kuma ya nuna yadda ya ke da karfin cin tsirrai.
Kawo yanzu dai an gano irin wannan kadangaren Dinosaurs mai gashi a jikinsa ne a kasar China, daga dabbobin da suke cin nama wadanda ake kira Theropods a turance.
Bincike na baya-bayan anan da aak gudanar a kasar Rasha, an gano shi ne daga a wurin kadangarun Dinosaurs da aka killace wadanda ba sa cin komai sai tsirrai, wanda hakan yake a kusan dukkannin kadangaru irinsu.

Matsalar Manhajar Android wajen Kariya

Aside

An gano matsalar manhajar Android da ke iya bayar da damar da za a iya kutse cikin bayanan katin dibar kudi na Banki na mai amfani da wasu manhajojin.
Kamfanin harkokin tsaro na intanet na BlueBox, ya ce manhajar Android ba ta cikakken bincike akan na’urorin kare kutse (IDs) kafin ta bai wa sauran manhajoji (Apps) dama ta musamman akan wayoyin komai-da-ruwanka da kananan kwamfutocin hannu.
Masu BlueBox suka ce matsalar ita ce masu wayoyin salula da kananan kwamfutoci na hannu na komai da ruwanka (Tablets) ba lalle sai sun bayar da izini ba, wata manhajar (Apps) take aiki a na’urorinsu.
Kamfanin ya ce ya sanar da Google tun da farko domin ya dauki matakan gyara manhajarsa (Operating System).
Google ya tabbatar cewa ya kirkiro abin da zai magance wannan matsala.
Mai magana da yawun kanfanin manhajar Android ta ce, suna godiya ga BlueBox da ya gano musu wannan matsala.
Ta ce, irin wannan bincike da wasu ke yi shi ne yake sanya wa Android ta na kara inganci.
Kuma ba tare da wani jinkiri ba suka aika da bayanan yadda za a kare matsalar ga abokanan huldar Android.
Har yanzu wasu wayoyin masu Android na fuskantar matsalar
Sai dai kuma har yanzu wadanda ke amfani da manhajar Android ta daga 2.1 zuwa ta 4.3 ba su samu hanyar magance matsalar ba.
Kuma wayoyin komai-da-ruwanka (Smart Phones) da kananan kwamfutocin hannu da ba su samu hanyar magance matsalar ba, na cikin hadari idan suka dauko wata manhaja ba daga rumbun Google Play Store ba.

BARKA DA SALLAH na MP3 JIBWIS Ring Tones. Danna Link domin Saukewa a Wayarka.

Aside

SYMHK Sautus Sunnah (Addu’a)

http://kiwi6.com/file/2gba3i7f5x

SMKH Gombe 2 (Mutuwar Malaman Sunnah)

http://kiwi6.com/file/qezsairw44h

JIBWIS CHAIRMAN (Mukaddima)

http://kiwi6.com/file/wd0u8wdas1

SAG Argungu 1 (Subhanallah)

http://kiwi6.com/file/zb8mrhxcpt

AHMAD SULEMAN (Addu’a)

http://kiwi6.com/file/ml3sw1unvd

SMKH Gombe (Waliyyi mai Piano)

http://kiwi6.com/file/tapmw7rjsh

ZRA006 SMKH GOMBE 1 (Kisan Albani + Ja’afar)

http://kiwi6.com/file/jzfj70hf78

ZRA006 SMKH GOMBE 2 (Kisan Albani)

http://kiwi6.com/file/vbc4xwneyu

ZRA006 SMKH GOMBE 3 (Kisan Albani)

http://kiwi6.com/file/l6oda4esr8

SMKH Gombe (Shawara ga yan bidia)

http://kiwi6.com/file/4dakdf5hue